in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a tattauna batutuwa masu dimbin yawa a yayin jerin manyan tarukan MDD karo na 71
2016-09-19 13:37:57 cri

A jajibirin kaddamar da jerin manyan tarukan MDD karo na 71, shugabanni ko wakilansu daga kasashe mambobin MDD 193 za su taru a birnin New York, inda hedkwatar MDD take. Ana fatan za a himmatuwa da nuna kuzari kan yadda za a aiwatar da ajandar neman dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 a yayin jerin manyan tarukan MDD, sannan za a iya bullo da dabarun tinkarar matsalolin 'yan gudun hijira, da hanzarta kaddamar da "yarjejeniyar Paris" domin tinkarar sauyin yanayin duniyarmu, da batun daidaita rikicin Sham da yaki da ta'addanci. Yanzu ga wani rahoton da abokin aikinmu Sanusi ya hada mana.

Bisa ajandar da aka tsara, za a yi muhawara a yayin tarurukan da za a yi a tsakanin ranakun 20 da 26 ga wannan watan da muke ciki, a dabra kuma da za a shirya wasu tarurukan da manyan jami'ai na kasashen duniya za su halarta. Alal misali, a ranar Litinin, 19 ga wata, za a shirya wani taron tattauna kan yadda MDD za ta tinkari matsalolin kai da kawon 'yan gudun hijira da masu cin rani a tsakanin kasa da kasa. Sannan a ranar Laraba, 21 ga wata, za a shirya bikin mika takardun amincewa da "yarjejeniyar Paris", sannan za a shirya taruka da dama game da batutuwan neman dauwamammen ci gaba da albarkatun ruwa da tsabtace muhallin al'umma da batun fama da matsalar yunwa da dai makamantansu.

Abin da ya kamata in ambato musamman shi ne, a yayin taruka, bisa shawarar bangaren kasar Sin, za a yi taron kara wa juna sani kan yadda za a aiwatar da shirin neman dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, inda za a bayyana sakamako da tunanin neman ci gaba da kasar Sin ta samu, domin kokarin fitar da sabbin matakan bunkasa harkokin al'ummomin duniya baki daya.

Bugu da kari, a yayin taron koli game da batun 'yan gudun hijira da masu cin rani, Mr. Ban Ki-moon, babban sakataren MDD da Mr. William Lacy Swing za su sa hannu kan "yarjejeniyar dangantaka dake tsakanin MDD da kungiyar 'yan cin rani ta kasa da kasa". Sakamakon haka, kungiyar 'yan cin rani ta kasa da kasa za ta zama wata mambar kungiyar MDD. Bugu da kari, bisa matsaya daya da kasashe 193 mambobin MDD suka cimma kwanan baya, za a zartas da wani kuduri a yayin taron, inda za su dauki jerin alkawura kan yadda za a daidaita matsalolin 'yan gudun hijira da 'yan cin rani, ana sa ran za a kafa wani tsarin mayar da marbani ga batutuwan 'yan gudun hijira da 'yan cin rani.

A kwanan baya, a lokacin da yake ganawa da 'yan jarida, Mr. Filippo Grandi, babban kwamishina mai kula da harkokin 'yan gudun hijira na MDD ya bayyana cewa, abin ya fi muhimmanci wajen warware matsalolin 'yan gudun hijira shi ne a yi kokarin kawo karshen rikice-rikicen da ke faruwa a wasu yankuna da kuma kawo zaman lafiya ba tare da kasala ba. Sannan ya kamata a yi kokarin tallafawa kasashe wadanda suke karbar 'yan gudun hijira. Ya jaddada cewa, kare 'yan gudun hijira baban alhaki ne ga al'ummomin duniya gaba daya.

Game da batun tinkarar sauyin yanayin duniya, a kwanan baya, kasashen Sin da Amurka sun mika wa MDD takardunsu na amince da "yarjejeniyar Paris". Sakamakon haka, sun taka muhimmiyar rawa matuka wajen ingiza "yarjejeniyar Paris" za ta iya fara aiki tun da wuri. A ranar Laraba, 21 ga wata, Mr. Ban Ki-moon zai shugabanci wani biki, inda zai gayyaci shugabannin kasashen duniya da su mika takardunsu na amincewa da yarjejeniyar din.

Manazarta suna ganin cewa, shugabannin ko wakilansu na kasashen duniya za su samu damar tattauna kan yadda za a warware matsalolin da suke jawo hankulan al'ummomin duniya baki daya a yayin wadannan jerin tarukan MDD. An labarta cewa, za a kuma shirya wasu taruka game da batun Sham da na batun makamashin nukiliya na Iran, da batun yaki da kungiyar IS da tunanin ta'addanci da batun kokarin kawar da nukiliya daga yankin Koriya da batun sake kaddamar da ayyukan shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya dai makamatansu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China