161005-Ziyarar-Souleymane-daga-Jamhuriyar-Nijar-a-nan-kasar-Sin-Sanusi.m4a
|
Ita dai wannan kungiya a wannan karo ta gayyato 'yan jaridu guda 28 daga kasashen Afirka ciki har da Jamhuriyar Nijar da kuma Najeriya, domin ganewa idonsu yadda kasar Sin ta ci gaba a fannonin tsaro, samar da horo, inganta harkokin kiwon lafiya, sufuri da sauransu.
Wannan wani bangare ne na hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da nahiyar Afirka. Kana wani sashe na alkawarin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi a lokacin taron kolin hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu dangane da taimakawa ci gaban nahiyar ta Afirka.
Yanzu haka, tawagar 'yan jaridun ta ziyarci birane da garuruwa na kasar Sin kimanin ashirin, baya ga ziyartar kamfanoni da masana'antu don shaida ci gaban da kasar Sin ta samu a fannoni dabam-dabam. Haka kuma 'yan jaridun sun halarci taron kolin G20 da ya gudana a birnin Hangzhou da ke nan kasar Sin.
Masana na cewa, wannan wata dama ce ga 'yan jaridun da suka ci gajiyar wannan shiri daga kasashe daban-daban na Afirka wajen amfani da abubuwan ci gaban da suka gani a kasashensu bayan sun koma gida.
Haka za lika, wannan wani mataki ne da ke kara tabbatar da aniyyar kasar Sin ta taimakawa ci gaban nahiyar Afirka daga dukkan fannoni. (Ibrahim, Souleymane, Sanisu Chen)