160921-An-kammala-taron-G20-a-birnin-Hangzhou-na-kasar-Sin-Sanusi.m4a
|
Masana na nuna cewa, an gudanar da taron kolin G20 na birnin Hangzhou ne a yayin da tattalin arzikin duniya ke kara fuskantar sauye-sauye, da kuma kokarin ganin an aiwatar da gyare-gyare kan kungiyar G20.
Mahalarta taron kolin G20 sun tsara shirin bunkasuwar cinikayya a duniya, da kuma takardar ka'idojin zuba jari ta G20, wanda ya zama tsarin zuba jari na farko na duniya, kana za a ci gaba da goyon bayan tsarin cinikayya a tsakanin kasashe daban daban, da kuma nanata alkawarin nuna adawa da ba da kariya ga tattalin arziki. Ana sa ran tattalin arzikin duniya zai samu farfadowa ta hanyar inganta cinikayya da zuba jari a duniya.
Masu fashin baki na cewa, bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, an cimma nasarar wannan taron da ya kasance mafi kayatarwa a tarihin kungiyar, kuma za a ci gaba da aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron, domin tabbatar da neman samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai dorewa. (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanisu Chen)