160916-bikin-tsakiyar-yanayin-kaka-lubabatu.m4a
|
Bikin Zhongqiu na daya daga cikin muhimman bukukuwan gargajiya na Sinawa, wanda a kan yi shi a ranar 15 ga wata na takwas bisa kalandar gargajiya na kasar Sin, wato ya fado a daidai tsakiyar yanayin kaka, shi ya sa ake kiranta bikin tsakiyar yanayin kaka. A wannan shekara, bikin ya fado daidai a ranar 15 ga watan Satumba. A lokacin bikin, wata ya kan cika, kuma ya fi da'ira da kuma haske, kuma a lokacin da jama'a ke hango duniyar wata, su kan fara kewan iyalansu, shi ya sa Sinawa sun dauki bikin a matsayin bikin haduwa da iyali. Wadanne al'adu ne a ke bi wajen gudanar da bikin? Ina ne ma'anar bikin ga Sinawa? Sai a biyo mu a shirin domin samun karin bayani.(Lubabatu)