in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da babban taron MDD karo na 71
2016-09-14 11:18:19 cri

A jiya Talata ne a hedkwatar MDD da ke birnin NewYork na kasar Amurka, aka kaddamar da babban taron MDD karo na 71. An kimmanta cewa, yayin taron, za a tattauna wasu batutuwan dake shafar cimma burin samun dauwamammen ci gaba a fadin duniya, da matsalolin 'yan gudun hijira da kasashen duniya ke fuskanta, da rikicin kasar Syria da dai sauransu.

Kafin a kaddamar da taron, sai da sabon shugaban babban taron MDD kana jakadan kasar Fiji Peter Thomson ya yi rantsuwar kama aiki.

Bana ita ce shekara ta farko da aka fara gudanar da ajandar samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, a saboda haka, aka sanyawa babban taron taken "Cimma burin samun dauwamammen ci gaba: kasashen duniya su yi kokari tare domin sauya duniyarmu."

A jawabinsa yayin bikin bude taron, Peter Thomson ya bayyana cewa, yana fatan wannan babban taron da ake gudanarwa zai sa kaimi kan kokarin da ake domin samun dauwamammen ci gaba. Thomson ya ce, "Wajibi ne mu fahimci cewa, har yanzu yawancin al'ummomin kasashen duniya ba su fahimci ajandar samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 sosai ba, shi ya sa ba su san abin da ya dace su yi domin cimma wannan burin da aka tsara a fannoni 17 ba. Muddin aka cimma wannan burin, to, hakika za a kawar da talauci a fadin duniya, tare kuma da samun dauwamammen ci gaban bil-Adama, bisa wannan dalili ne, aka mayar da batun 'kasashen duniya su yi kokari tare domin sauya duniyarmu' a matsayin taken wannan babban taron."

Ajandar samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 ta kasance babban sakamakon da MDD ta samu a cikin 'yan shekarun da suka gabata. A yayin taruruwan kolin da aka yi domin murnar cika shekaru 70 da kafa MDD, shugabannin kasashen duniya sun zartas da wannan ajanda dake kunshe da manyan ayyuka 17 a hukumance. Ajandar tana da babbar ma'ana saboda ita ce takardar dake shafar neman samun dauwamammen ci gaba da dukkanin kasashen duniya suka zartas da ita a karo na farko a tarihin bil-Adama.

A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin ta riga ta fara aiwatar da wannan ajandar samun dauwamammen ci gaba, kuma za ta gabatar da shirin da ta tsara game da wannan ajandar a yayin babban taron, kasar Sin ta yi hakan ne domin tana son nuna wa kasashen duniya irin matakan da ta dauka domin cimma burin nan na samun dauwamammen ci gaba, da kuma sakamakon da ta samu a wannan fannin.

Ban da wannan kuma, a yayin taron kolin G20 da aka kammala a birnin Hangzhou na kasar Sin, kasar Sin ta bukaci kasashe mambobin kungiyar G20 da su tsara shirin da zai tabbatar da ajandar ci gaba nan da shekarar 2030, wannan shirin zai taimaka wajen aiwatar da ajandar. Babban sakataren MDD Ban Ki-moon shi ma ya yaba da kokarin da kasar Sin ta yi kan wannan batu.

Game da rawar da kasar Sin ta taka a aikin aiwatar da ajandar ci gaba nan da shekarar 2030, shugaban hukumar da ke nazari kan manufofin ci gaban tattalin arziki da harkokin zaman takewar al'umma ta MDD Hong Pingfan ya bayyana cewa, manufofin da kasar Sin ke aiwatarwa, kamar shirin "ziri daya da hanya daya" da sauransu sun dace sosai da manufar ajandar ci gaba nan da shekarar 2030. Hong Pingfan ya ce, "Ko da yake akwai banbanci a tsakanin shirin ziri daya da hanya daya da ajandar ci gaba nan da shekarar 2030, amma burinsu daya ne, suna martaba ka'idojin MDD, suna kuma kokarin samun ci gaba da wadata tare, ana iya cewa, manufofinsu iri daya ne."

Kazalika, za a kaddamar da taron kolin MDD kan batun 'yan gudun hijira a ranar 19 ga wata, yayin taron, za a tattauna kan yadda za a dauki matakai domin dakile matsalolin da ake fuskanta a wannan fannin.

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, taron koli kan batun 'yan gudun hijira da za a gudanar yana da muhimmanci matuka

Shugaban babban taron MDD Thomson ya jaddada cewa, wajibi ne kasashen duniya su sauke nauyi da ke kansu domin daidaita matsalar 'yan gudun hijira yadda ya kamata. Ya ce, "Na ji bakin ciki kwarai yayin da na ga wasu kasashe suna nuna halin ko-in kula ga 'yan gudun hijira wadanda suka rasa muhallansu bisa dalilin rikici ko sauyin yanayi. Ina kuma yabawa kasashen da suke samar da taimako ga 'yan gudun hijira."

Wasu sabbin alkaluma na nuna cewa, kawo yanzu adadin 'yan gudun hijira a fadin duniya ya kai biliyan 60, kuma kashi 90 cikin dari daga cikin wannan adadi sun shiga kasashe masu tasowa.

Kana yayin wannan babban taron, ana fatan za a tattauna batun rikicin Syria.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China