in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude gasar Olympics ta nakasassu a Brazil
2016-09-15 11:35:18 cri

A ranar Laraba 7 ga watan Satumban shekarar 2016 ne aka bude gasar wasannin Olympics ta nakasassu a birnin Rio na kasar Brazil. 'Yan wasa 4,350 daga kasashe fiye da 160 ne sun fafata a wasanni 23 a cikin kwanaki 11 ana barje gumi.

An kebe lambobi 225 da mata za su lashe a wannan gasa, yayin da aka kebe lambobi 265 da maza za su lashe, sai kuma wasu lambobi 38 na mai rabo ka dauka wato mace ko namiji za su iya lashewa a lokacin gasar.

Bayanai na nuna cewa, an samu karin mata a gasar ta bana idan aka kwatanta da gasar da ta gudana a birnin London, inda adadin ya kai kashi 10 cikin 100.

Kamar babbar gasar Olympics da aka kammala a birnin Rio na kasar ta Brazil ba da dadewa ba, ita ma wannan gasa ta gamu da matsalar karancin kudi, abin da ya sa masu shirya gasar suka soke wasu abubuwa da aka tsara gudanarwa a baya.

Masu fashin baki na cewa, wannan wata dama ce ga nakasassu su nuna irin basirar da Allah ya hore musu, baya ga fito da sunayen kasashensu a fagen wasanni ta wannan gasa.

Sai dai 'yan wasan kasar Rasha ba za su shiga wannan gasa ba, sakamakon haramcin da aka kakaba musu saboda zargin 'yan wasan kasar ta Rasha da amfani da kwayoyin da ke kara kuzuri. Koda ya ke kasashe Sin, Afirka da sauran kasashe sun tura tasu tawagar da za su fafata a gasar Olympics ta nakasassun karo na 15 da ke gudana a birnin Rio na kasar Brazil.

Masana dai na cewa, damawa da nakasassun a fagen wasanni, wata dama ce ta magance matsalar barace-barace ko zaman kashe wando da wasu nakasassun ke yi, duk da kokarin da hukumomi ke yi na inganta rayuwarsu daga dukkan fannoni. (Saminu, Ada, Ibrahim/Sanisu Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China