in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar wakilin matasan Nijeriya Muhammad Nazeef Sani a nan kasar Sin
2016-09-15 11:35:05 cri

Kwanan baya ne aka kaddamar da shagali na kwanaki hudu na bikin matasan Sin da Afirka na shekarar 2016, a birnin Guangzhou dake nan kasar Sin, bikin da ya zama wani bangare na aiwatar da shirin ziyarar juna a tsakanin matasan Sin da Afirka, wanda da aka cimma kudurin aiwatarwa, yayin taron kolin Johannesburg na FOCAC da ya gudana a watan Disambar shekarar bara.

Rahotanni sun nuna cewa wakilai 188, daga kasashen Afirka 18 ne suka halarci wannan shagalin biki na birnin Guangzhou, inda suka yi musayar ra'ayoyi da takwarorinsu su 200, wadanda ke zaune a lardin Guangdong a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da al'adu, da hidimar zaman takewar al'umma da dai sauransu.

Haka kuma, kafin gudanar wannan shagali na birnin Guangzhou, an yi bikin wake-wake da raye-raye na matasan kasashen Asiya da Afirka karo na farko a nan birnin Beijing, inda matasa 600 daga bangarorin siyasa, da kafofin watsa labaru, da kasuwanci, da nazari daga kasashen Asiya, da na Afirka 36, suka taru a nan kasar Sin domin yin mu'amala, da kara fahimtar juna a tsakaninsu. Bayan hakan ne kuma, wakilai 188 daga kasashen Afirka, suka ci gaba da ziyarar da suke gudanarwa a nan kasar zuwa birnin Guangzhou, inda aka yi shagalin biki na matasan Sin da Afirka a can.

Wakiliyar sashen mu Kanda Gao ta halarci wannan bikin da aka yi a Guangzhou, inda ta zanta da wasu wakilan matasan Afirka, cikin hada dan Najeriya malam Muhammadu Nazeef Sani, inda suka tattauna kan tasirin wannan ziyara ta sa a kasar Sin, da yadda biranen Sin suke burge shi, da kuma matsayi na matasa a cikin harkokin ci gaban kasashe da dai sauransu. Ga kuma rahoton da Kande ta hada mana:

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China