in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron kasar Sin ya halarci taron ministoci na MDD kan batun kiyaye zaman lafiya
2016-09-09 09:29:27 cri
Ministan tsaron kasar Sin Mista Chang Wanquan ya halarci taron ministoci na MDD kan batun kiyaye zaman lafiya da aka kira a jiya Alhamis a birnin London tare da ba da jawabi.

A cikin jawabinsa, Mista Chang ya bayyana cewa, a gun taron koli kan batun kiyaye zaman lafiya da MDD ta kira a shekarar 2015, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dauki alkawura guda shida don nuna goyon baya ga karfafa karfin kiyaye zaman lafiya na MDD, matakin da ya bayyana gudunmawar da Sin ke bayar a matsayin wata kasa mai karfi wajen kiyaye zaman lafiya da na karko a duniya. Gwamnatin Sin da kuma sojinta sun riga sun horar da ma'aikatan kiyaye zaman lafiya 500 na kasashe daban-daban, kuma nan ba da dadewa ba za ta kammala yin rajistar sojojin kiyaye zaman lafiyarta kimanin 8000 a MDD, ban da wannan kuma, rukunin jiragen sama masu saukar ungulu na kiyaye zaman lafiya na farko da Sin ta kera za a tura shi zuwa wuraren da ake bukata.

Mista Chang kuma ya nanata cewa, Sin tana nacewa ga hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, kuma tana dukufa kan kiyaye zaman lafiya. A cikin shekaru 26 da suka gabata, Sin ta tura sojoji dubu 33 don su gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya na MDD. Ya kara da cewa, a cikin shekaru uku masu zuwa, Sin za ta dauki nauyinta na biyan kudin kiyaye zaman lafiya na kashi 10.2 bisa dari na MDD. Ban da wannan kuma Sin za ta ci gaba da cika alkawarinta na kiyaye zaman lafiya da nuna himma da gwazo kan wannan aiki, tare kuma da gudanar da hadin gwiwa da kasashen daban-daban a wannan fanni. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China