160902-taron-kolin-G20-Lubabatu.m4a
|
Za a kira taron kolin kungiyar G20 a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin daga ran 4 zuwa 5 ga wannan wata. Taken taron shi ne "Shimfida yanayin tattalin arzikin duniya bisa kirkire-kirkire, kuzari, da hadin gwiwa". Shugabannin kasashe membobin kungiyar ta G20 da shugabannin kasashen da aka gayyata da kuma jami'an kungiyoyin kasa da kasa masu ruwa da tsaki ne za su halarci taron.
Shin wadanne abubuwa ne za a tattauna a gun taron, kuma yaya taron zai amfana wa kasashen Afirka? A kasance tare da mu a shirin domin samun karin haske.(Lubabatu)