A jiya Alhamis ne wani roka kirar Falcon 9 da kamfanin SpaceX na kasar Amurka ya kera ya fashe a yayin da ake gwajinsa. Ko da yake babu wanda ya mutu ko ya jikkata sakamakon lamarin, amma hakan ya sake nuna irin koma bayan da Amurka ta samu a sana'ar kasuwancin sararin samaniya.
Rokan ya fashe ne a sansanin sojojin sama na Cape Canaveral da ke jihar Florida ta Amurka. Sanarwar da kamfanin SpaceX ya bayar, ta tabbatar da cewa, an gamu da matsala a yayin da ake shirya gwajin harba rokar kirar Falcon 9, wanda ya haddasa fashewa da kuma lalacewar rokar, har ma da tauraron dan Adam din baki daya..
A halin yanzu dai, sojojin saman Amurka sun dauki matakan killace sansanin don hana mutane shiga cikinsa.
A karshen wannan mako ne dai aka shirin harba rokar kirar Falcon 9, wadda ke dauke da wani tauraron dan Adam na kasar Isra'ila.(Kande Gao)