in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta shirya karbar bakuncin takon kolin G20 na bana
2016-09-02 10:02:43 cri

Yanzu haka dai birnin Hangzhou da ita kanta kasar Sin sun shirya tsaf don karbar bakuncin taron koli karo na 11 na kungiyar G20 da za a bude a ranar 4 zuwa 5 ga watan Satumban wannan shekara ta 2016 a Hangzhou. Kuma shugabannin kasashen Amurka da Rasha da Faransa da kasar Afirka ta Kudu na daga cikin wadanda za su halarci wannan taro.

Sauran sun hada da firaministocin kasashen Birtaniya da Indiya da Japan da shugaban majalisar EU Donald Tusk‎, da shugaban hukumar kula da harkokin EU Jean-Claude Juncker, akwai kuma shugabannin kasashen Argentina, Brazil, Indonesiya, Koriya ta Kudu, Mexico, Turkiyya, Australia, Canada, Jamus, Italiya, Saudiyya wadanda za su halarci taron a matsayinsu na shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20.

Haka kuma, shugaban kasar Chadi Idriss Déby, da shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi, da shugaban kasar Senegal Macky Sall, da shugabannin kasashen Kazakhstan, Laos, Singapore, Spaniya, da Thailand za su halarci taron ne a matsayin kasashe baki da aka gayyata.

Bugu da kari, taron zai kuma samu halartar wasu shugabannin kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da babban sakataren MDD Ban ki-Moon, da shugaban bankin duniya Kim Jim-Yong, da shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF Christine Lagarde, da babban daraktan kungiyar WTO Roberto Azevedo, da kuma shugabannin kungiyar kwadago ta duniya ILO, da kwamitin ba da tabbaci ga harkokin kudi FSB, kana da kungiyar hadin kan tattalin arziki don ci gaba OECD da dai sauransu.

Masana na ganin cewa, wannan wata babbar dama ce ga kasar Sin ta nunawa duniya irin matakan da take dauka na bunkasa tattalin arzikinta, ta yadda sauran kasashen duniya ciki har da kasashen Afirka za su yi koyi da su, domin ceto halin da tattalin arzikin duniya ya tsinci kansa a ciki yanzu haka.

Taken taron na bana dai shi ne shimfida yanayin tattalin arzikin duniya mai kirkire-kirkire, kuzari, da kuma hadin gwiwa. (Souleymane, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China