in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Japan tana zawarcin kasashen Afirka domin cimma wata manufa
2016-08-29 11:31:50 cri

A ranar 27 zuwa 28 ga wata ne, Japan ta kira taron raya Afirka na kasa da kasa karo na shida a Nairobi, hedkwatar mulkin kasar Kenya, taron da ya samu halartar firaministan kasar Japan Shinzo Abe. Wannan ne karo na farko da kasar Japan ta shirya wannan taro a Afirka. A cewar kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP, Japan ta yi hakan ne domin nuna wa duniya cewa, wai tana taimakawa kasashen Afirka ne. Bugu da kari, manazarta sun nuna cewa, ko da Japan ta nuna aminci ga Afirka, amma a bayyane take cewa, ta boye manufofinta na tattalin arziki da siyasa a baya, gami da makircinta na neman fadada karfinta ta fuskar soja a ketare bisa hujjar hada kai tare da kasashen Afirka.

Kasar Japan ce ta shugabanci taron kasa da kasa don neman ci gaban Afirka da aka shirya a kasar ta Kenya. Kuma tun lokacin da aka kaddamar da shi a shekarar 1993, sannu a hankali, taron ya kasance kashin bayan ayyukan diplomasiyya tsakanin Japan da kasashen Afirka. Tun daga taron Kenya na wannan shekarar da muke ciki, za a takaita lokacin kira taron zuwa ko wadanne shekaru uku, wanda a baya a kan shirya shi a ko wadanne shekaru biyar, lamarin da ya sheda muhimmancin da Japan ta kara dora wa kasashen Afirka.

Japan ta fara baiwa kasashen Afirka taimako ne tun a shekarar 1966. Tun bayan da aka gamu da matsalar hauhawar farashin man fetur fiye da kima a shekaru 70 na karnin da ya gabata, Japan ta kara mai da hankali kan Afirka, wadda ke da albarkatun man fetur. Kuma tun daga wancan lokaci ne, gwamnatin Japan ta kara baiwa kasashen na Afirka taimako. Har ma a farkon shekaru 90 na karnin da ya gabata, Japan ta kasance kasa mafi girma ta biyu da ke baiwa Afirka tallafi bayan kasar Faransa.

Bayan da aka shiga sabon karni na 21, Japan ta kara dora muhimmanci matuka ga Afirka bisa manyan tsare-tsare. Kafin wannan kuma, tsoffin firaministocin kasar Yoshiro Mori da Junichiro Koizumi sun taba ziyarar kasashen Afirka daya bayan daya.

Manazarta na ganin cewa, Japan tana kara inganta harkokinta na diplomasiyya a Afirka ne, saboda wasu manufofinta na musamman.

Na farko, Japan ta kara samar da taimako ga Afirka ne domin wata manufa ta siyasa, wato tana fakewa da batun taimako domin neman goyon baya a siyasance. Kamar yadda aka sani, yawan kasashen Afirka ya kai rubu'i kasashen mambobin Majalisar Dinkin Duniya, kuma tun bayan kafuwar kungiyar tarayyar Afirka AU a shekarar 2002, kasashen Afirka na taka muhimmiyar rawa a cikin lamuran kasa da kasa. Wani masanin kasar Sin a fannin nazarin kasar Japan ya taba hasashen cewa, babu shakka Japan tana da aniyar nuna matsayinta na kasancewa kasa mai karfi a siyasance, matakinta na neman goyon baya daga wajen kasashen Afirka, hakan zai iya taimaka mata wajen yada manufofinta da tunaninta gami da salonta na raya kasa, a kokarin cimma burinta na zama wata mamba ta din din din a kwamitin sulhu na MDD.

Ban da haka kuma, idan muka dubi ayyukan da suka shafi tattalin arziki da ci gaban makamashi, to za mu iya gano cewa, Japan na neman mayar da Afirka a matsayin ginshikin cimma nasarar manufarta ta zama wata kasa mai karfin takara a duniya. Japan kasa ce da ta shahara a fannin masana'antu wadda take da karancin makamashi sosai. A halin yanzu dai, kashi 85 cikin kashi dari na yawan gurbataccen man fetur da Japan ke bukata yana zuwa ne daga yankin gabas ta tsakiya, amma sakamakon tashe-tashen hankalin da ke abkuwa a yankin, ana fuskantar hadari sosai wajen samun makamashi daga wurin. Don haka, idan Japan tana son kara fadada hanyoyinta na samun man fetur, to Afirka da ke da arzikin albarkatun kasa da makamashi wani zabi ne mai kyau sosai.

Haka zakila, bisa abubuwan da Japan ke yi, ana iya gano makircinta na neman fadada matsayinta ta fuskar soja a ketare. A shekarar 2009, ta sake fakewa da batun dokar tinkarar 'yan fashin teku, inda gwamnatin Japan ta ari wasu yankuna daga kasar Djibouti don kafa sansanin rundunar sojojin tsaron kanta, wai don ta tinkari matsalar 'yan fashin teku da ke Somaliya da mashigin tekun Aden. Sa'an nan a shekarar 2011, an kaddamar da wannan sansani, wanda ya kasance sansani daya tak da rundunar sojojin tsaron Japan ta ke da shi a ketare.

A yayin taron kasa da kasa na Tokyo karo na biyar da aka kira a shekarar 2013, wani jami'in gwamnatin kasar Mauritius da ya halarci taron ya furta cewa, abin da Afirka ke bukata shi ne sahihan abokai, a maimakon 'yan fashi. Don haka, har yanzu wasu kasashen Afirka na yin taka tsantsan kan irin babban taimakon da Japan ke samar musu. Idan Japan na da aniyar zawarcin Afirka, to ya kamata ta yi watsi da manufofinta da ta boya a baya, ta kuma nuna sahihanci da abin da ke zuciyarta a fili ga Afirka, tare da aniyar taimakawa Afirka don samun ci gaban mai dorewa da kuma yadda hakan zai amfana wa jama'arta.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China