in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala gasar Olympics ta Rio
2016-08-25 14:16:32 cri

A ranar Lahadi 21 ga watan Agustan shekarar 2016 ne aka kammala gasar wasannin Olympics da aka gudanar a birnin Rio na kasar Brazil, kana gasar Olympics ta farko da aka gudanar a yankin kudancin nahiyar Amurka.

'Yan wasa dubu 11 da 400 daga kasashe da yankuna 207 ne suka fafata a wasanni 39, inda aka lashe lambobi 78, 'yan jaridu dubu 25 da masu yawon shakatawa sama da miliyan 1 ne suka halarci gasar da aka shafe kwanaki 16 ana fafatawa.

Kasar Amurka ce ka kasance a kan gaba wajen lashe lambobi, sai Burtaniya ta biyu kana kasar Sin ta zo ta uku, yayin da Brazil mai masaukin baki ta zo ta 13. A bangaren nahiyar Afirka kuwa, kasar Kenya ce ja gaba da lambobin yabo 13. Kana a cikin kasashen Afirka 11 da suka lashe lambobi, akwai Nijar mai azurfa 1 wadda ita ce lamba ta farko da kasar ta samu a kusan tsawon shekaru 30, Najeriya kuma ta samu tagulla 1, lamarin da ya janyo cece-kuce game da rawar da Najeriyar ta taka a wannan gasa.

Bugu da kari, su ma kasashen Habasha da Afirka ta kudu da sauran kasashen Afirka sun taka rawar gani a wannan gasa inda suka lashe lambobin yabo daban-daban a wasannin da suka fafata.

Kafin gasar ta Rio dai, an yi ta nuna shakku kan kasar ta Brazil na shirya wannan gasa, sakamakon zanga-zangar da 'yan kasar suka yi ta gudanarwa na nuna rashin amincewarsu da daukar bakuncin gasar, saboda abin da suka kira, halin matsin da ake ciki a kasar da kuma makuden kudaden da aka ware don shirya wannan gasa, baya ga batun cutar Zika da masana kiwon lafiya a baya suka ba da shawarar dauke gasar daga Brazil zuwa wata kasa ta daban da dai sauransu.

A karshe dai an kammala wannan gasa cikin nasara, inda 'yan wasa a fannoni daban-daban suka sake kafa gajinta, wasu kuma suka kare kambunsu, yayin da wasu kuma suka kasa kare nasu kambun.

Masu sharhi na fatan cewa, wata rana za a shirya wannan gasa a nahiyar Afirka duk da cewa, gasa ce da ke bukatar kudade, matakan tsaro da wasu tanade-tanade da kwamitin IOC ke gindayawa kafin kasa ta kai ga samun sanasar karbar bakuncin gasar da watakila za su yiwa nahiyar wahalar cikawa. (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China