160823-hadin-gwiwa-a-tsakanin-sin-da-nijeriya-na-da-makoma-mai-haske-Maryam.m4a
|
Jama'a assalam alaikum! Barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan sabon shiri na SIN DA AFRIKA, ni ce Maryam tare da Saminu Alhassan muke gatabar muku da shirin daga nan sashin Hausa na gidan rediyon kasar Sin wato CRI dake nan birnin Beijing.
Kwanan baya, wata tawagar wakilan gwamnatin kasar Nijeriya dake hada da wasu manyan jami'an kasar ta kai ziyara a nan kasar Sin domin yin shawarwari da takwarorinsu na Sin da kuma ziyarci wasu kamfanoni da wuraren kasar da abin ya shafa, ta yadda za a iya habaka harkokin hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu, malam Saminu ya zanta da wasu daga cikinsu, inda suka bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya tana fuskar makoma mai haske, ga kuma rahoton da ya hada mana: