Wang Yi, ministan harkokin waje na kasar Sin ya ce, kasancewar Sin da Japan, da kuma Koriya ta kudu kasashe masu karfin tattalin arziki a gabashin nahiyar Asiya, suna daukar babban nauyi ta fuskar raya tattalin arziki, da hadin gwiwa da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar.
Wang Yi ya kara da cewa, Sin za ta gudanar da taron kolin kungiyar G20 a birnin Hangzhou, a matsayinsu na muhimman mambobin kungiyar G20, kasar Sin tana fatan kara tuntubar juna da hadin gwiwa da Japan da Koriya ta kudu, ta yadda taron zai ba da taimako ta fannin raya tattalin arzikin duniya da kuma inganta tsarin tattalin arzikin duniya.(Lubabatu)