in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar AU ta yi alkawarin dakile Al-Shabaab dake neman hana zabuka a Somaliya
2016-08-24 10:19:35 cri

Wani jami'in kungiyar tarayyar Afrika (AU) dake kasar Somaliya ya bayyana a ranar Talata cewa, tagawar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika dake Somaliya (AMISOM) za ta yi aiki tare da sojojin Somaliya wajen ba da kariya domin dakile mayakan Al-Shabaab dake neman hana gudanar da zabuka masu zuwa a kasar. Mataimakiyar manzon musammun ta shugabar kwamitin kungiyar AU game da kasar Somaliya, Lydia Wanyoto, ta yi wannan furuci a yayin wani zaman taro na shirya zabuka.

Kasar Somaliya ta kafa wani kwamitin aiki kan tsaro domin taimakawa wajen ba da kariya ga shirin zabuka da aka tsaida shiryawa a cikin watannin Satumba da Oktoba.

AMISOM za ta shiga cikin wannan kwamitin aiki. Somaliya za ta shirya wani takaitaccen zabe, da wasu al'ummomin kasar ba za su shiga ba. Wata tawagar zabe a karkashin hannun MDD, ta sanar a baya bayan nan cewa, za a gudanar da wani zaben shugaban kasa a ranar 30 ga watan Oktoba, kana kuma zaben 'yan majalisa daga ranar 24 ga watan Satumba zuwa 10 Oktoba.

Komandan dakarun AMISOM, Osman Noor Soubagleh, ya bayyana cewa, taron zai taimaka wajen gudanar da ayyukan yaki da kungiyar Al-Shabaab, dake kai hare haren ta'addanci lokaci zuwa lokaci a cikin wannan kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China