160809-An-kaddamar-da-shagalin-biki-na-matasan-Sin-da-Afirka-na-shekarar-bana-a-Guangzhou-Maryam.m4a
|
A ranar 2 ga watan nan da muke ciki ne, aka kaddamar da shagalin kwanaki hudu na bikin matasan Sin da Afirka na shekarar 2016, a birnin Guangzhou na nan kasar Sin, bikin da ya zama wani bangare na aiwatar da shirin ziyarar juna a tsakanin matasan Sin da Afirka, wanda da aka cimma kudurin aiwatarwa, yayin taron kolin Johannesburg na FOCAC da ya gudana a watan Disambar shekarar bara.
Rahotanni sun nuna cewa wakilai 188, daga kasashen Afirka 18 ne suka halarci wannan shagalin biki na birnin Guangzhou, inda ake fatan matasan za su yi musayar ra'ayoyi da takwarorinsu su 200, wadanda ke zaune a lardin Guangdong a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da al'adu, da hidimar zaman takewar al'umma da dai sauransu.
Haka kuma, kafin gudanar wannan shagali na birnin Guangzhou, an yi bikin wake-wake da raye-raye na matasan kasashen Asiya da Afirka karo na farko a nan birnin Beijing, inda matasa 600 daga bangarorin siyasa, da kafofin watsa labaru, da kasuwanci, da nazari daga kasashen Asiya, da na Afirka 36, suka taru a nan kasar Sin domin su yi mu'amala, da kara fahimtar juna a tsakaninsu. Bayan hakan ne kuma, wakilai 188 daga kasashen Afirka suka ci gaba da ziyarar da suke gudanarwa a nan kasar zuwa birnin Guangzhou, inda aka yi shagalin biki na matasan na Sin da Afirka a can.
Wakiliyar sashen mu Kanda Gao ta halarci bikin na birnin Guangzhou, inda ta zanta da wasu wakilan Afirka, cikin hada dan Najeriya malam Aminu Bello, ga kuma rahoton da ta hada mana.