in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A karon farko an fara amfani da na'urar dumama daki mai amfani da karfin iska a yankin Xinjiang
2016-08-08 14:04:15 cri

An yi amfani da na'urar dumama daki mai amfani da karfin iska irinta ta farko a birnin Dabancheng dake jihar Xinjiang, matakin da ya alamanta cewa yankin Xinjiang ya fara amfani da irin wannan na'ura a karo na farko.

Bayan an kammala wannan na'ura, za a yi amfani da ita wajen dumama dakuna da fadinsu ya kai cubic mita dubu 200 a yanayin sanyi, ta hanyar amfani da wutar lantarki da aka samar bisa karfin iska na kilowatt-hour miliyan 2.88, matakin da za a iya yin tsimi kwal ton 9158, wato an rage fitar da hayaki ton 25940 da dai sauran abubuwan da ke gurbata iska kimanin ton 1652. Matakin da ya kasance wani abin koyi wajen kyautata zamantakewar al'umma, kiyaye muhalli, da sa kaimi ga samar da cikakken wutar lantarki ga yankin Xinjiang, da kara yin amfani da makamashi mai tsafta. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China