160803-Rawar-da-Burtaniya-ta-taka-a-yakin-Iraki-Sanusi.m4a
|
Shugaban kwamitin John Chilcot wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce daukar matakin soja ba shi ne matakin karshe da ya dace a dauka a yakin na Iraki ba.
Bugu da kari, kwamitin binciken ya gano cewa, firaministan Burtaniya na wancan lokaci Tony Blair ya shaidawa tsohon shugaban Amurka George W. Bush watanni da dama kafin su kaddamar da shirin mamaye kasar Iraki cewa, yana tare da shi a kowane hali dangane da kasar ta Iraki.
Sai dai Tony Blair ya tsaya kai da fata cewa, shi fa ba shi ne ya yaudari Burtaniyar shiga yakin na Iraki da Amurka ta jagoranta ba. Kuma har zuwa wannan lokaci Blair ya ce, bai yi da-na-sanin sanya hannu wajen tunbuke gwamnatin tsohon shugaban Iraqin Saddam Hussaini ba, kuma ko yanzu ne zai sake daukar irin wannan hukunci.
Shi kuma tsohon shugaban sashen sadarwa ga tsohon firaiministan Burtaniya Alistair Campbell, ya soki Amurka da cewa, babu wani abun a zo a gani da Amurkar za ta ce ta cimma bayan mamaye kasar ta Iraki.
Bugu da kari, Janar Tim Cross, babban jami'in da ya tsara shigar da Burtaniya kawancen Amurka na mamaye Iraqi, ya ce Amurkar ce ta daidaita dakarun kasar ta Iraqi.
Wakilin Burtaniya a majalisar dinkin duniya na wannan lokacin, Jeremy Greenstock, ya amince da cewa Amurka ce ta yi wa Burtaniya shigo-shigo ba zurfi wajen yin amfani da karfin soji a Iraqi.
Masu fashin baki na cewa, kamata ya yi a ce masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya su samu isasshen lokaci wajen bincike da gano makamai masu gubar da aka ce Iraqin na da su a wancan lokaci kafin ma a kai ga daukar matakan soja.
Mahukuntan Amurka dai na cewa, yanzu haka manufar kasar ita ce samar da zaman lafiya tare da karya lagon kungiyar masu jihadi ta IS, dake kasar ta Iraki.
Sai dai kuma Amurkar ta amince cewa, duk da cewa an samu matsaloli sakamakon mamaye Iraki, amma duniyar ta fi dadi da aka kawar da Saddam Hussain.
A shekarar 2003 ne Burtaniya ta shiga kawancen Amurka na yaki a Iraqi, a inda ta tura dakaru 28,000. Ko da yake da dama daga cikin dakarun kasar sun kwanta dama a fagen yaki, baya ga wadanda suka jikkata.
Amurka dai ta bayar da dalilan kasancewar makamai masu guba a Irakin, a matsayin makasudin mamaye kasar, al'amarin da ya yi sanadiyyar rayukan mutane da dama da kuma tumbuke shugaba Saddama Hussain daga mulki, wanda daga bisani aka zartar masa da hukuncin kisa ta hanyar ratayewa. (Ahmed/Ada/Ibrahim/Sanisu Chen)