Taron wanda gwamnatin Rwanda tare da hadin gwiwar kungiyar kasashen gabashin Afirka da kungiyar kare muhalli ta kasa da kasa suka shirya, wata dama ce ta kare gandayen daji da ke kokarin bacewa a nahiyar Afirka sakamakon matsalar canjin yanayi.
Bayanai na nuna cewa, kasashen Afirka suna daga cikin yankunan da matsalar canjin ta fi shafa a duniya, duk da cewa nahiyar ba ta cikin yankunan da ke haddasa matsalar gurbatar yanayi a duniya.
Tun a makon da ya gabata ne mahalartar taron daga nahiyar ta Afirka suka hallara a birnin na Kigali inda suka bayyana kudurinsu na aiwatar da yarjejeniyar Bonn ta kare Eka miliyan 150 na gandun daji da filayen da aka yi watsi da su ya zuwa shekarar 2020 da kuma eka miliyan 350 ya zuwa shekarar 2030. (Ibrahim)