in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kira taron kolin CEMAC a Asabar mai zuwa a Malabo
2016-07-27 10:33:24 cri

Shugabannin kasashe mambobi na kungiyar tattalin arziki da kudi ta tsakiyar Afrika (CEMAC), za su yi wani taron musamman a ranar Asabar mai zuwa a birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea, in ji hukumar shiyyar a ranar Talata.

Wadanda ake jiran zuwansu a babban birnin na Equatorial Guinea, sun hada da shugabannin Denis Sassou N'Guesso na Congo, Idriss Deby Itno na Chadi, Ali Bongo Ondimba na Gabon, Faustin-Archange Touadera na Afrika ta Tsakiya, Paul Biya na Kamaru da kuma mai masaukin bakin nasu, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, domin bikin bude taron, da zai kuma biyo da shawarwari da tarukan.

Wannan taro zai gudana bisa kiran shugaba mai ci na kungiyar CEMAC, kuma shugaban Equatorial Guinea, mista Obiang Nguema Mbasogo.

Sake gina kasar Afrika ta Tsakiya da tattaunawa kan yarjejeniyar huldar dangantakar tattalin arziki (APE) tsakanin kasashen CEMAC da kungiyar tarayyar Turai za su kakace batutuwan wannan haduwa ta Malabo.

Haka kuma a kan teburin tattaunawar shugabannin na CEMAC, akwai maganar matsalar tattalin arziki dake gurgunta kasashen wannan shiyya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China