in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar Sin da Afirka zai bunkasa dunkulewar kasashen Afirka
2016-07-28 09:03:34 cri

A gabar da kasashen nahiyar Afirka ke daukar matakan ganin dunkulewar nahiyar waje gudu, mahukuntan kasar Sin sun bayyana aniyar su ta kaddamar da wasu tsare tsaren hadin gwiwa, wadanda za su tallafawa manufar wannan manufa.

A shekarar da ta gabata ne gwamnatin kasar Sin ta bayyana wasu kudurorin ci gaba 10, masu nasaba da hadin gwiwar Sin din da kasashen Afirka, yayin taron dandalin hadin gwiwar sassan biyu da ya gudana a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu, kudurorin da ake fatan ganin an cimma nasarar aiwatar da su cikin shekaru uku masu zuwa.

Wadannan kudurori dai sun kunshi bunkasa fannin noma na zamani, da samar da ababen more rayuwa, da bunkasa masana'antu, da fadada hada hadar kudade, da inganta fannin cinikayya da zuba jari. Sauran sun hada da samar da makamashi mai tsafta, da wanzar da zaman lafiya da tsaro, da yaki da talauci, tare da inganta rayuwar jama'a. Sai kuma batun habaka kiwon lafiya da musaya tsakanin al'umma.

Kaza lika bisa wannan aniya, kasar Sin ta ware kudi har dalar Amurka biliyan 60, domin tabbatar da an aiwatar da wadannan kudurori cikin nasara.

Game da hakan ne ma ministan hada-hadar kudi da raya tattalin arzikin kasar Rwanda Claver Gatete, ya bayyana cewa, hadin kan Sin da nahiyar Afirka ta fuskar raya sassan tattalin arziki, zai taka muhimmiyar rawa wajen cimma nasarar dunkulewar nahiyar. Mr. Gatete wanda ya bayyana hakan yayin zantawar sa da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ya ce, wadannan manufofi na tattalin arziki, da ma sauran matakai na ganin an cimma nasarar dunkulewar yankunan nahiyar Afirka wuri guda, za su taka muhimmiyar rawa wajen dunkulewar Afirka.

A daya hannun, ministan ya bayyana manufar hade sassan harkokin cinikayyar nahiyar bai daya, a matsayin daya daga manufofin da tuni shuwagabannin nahiyar suka dade suna maida hankali a kai, wanda kuma hakan zai baiwa nahiyar damar fadada hanyoyin ta na zuba jari, da kuma inganta matsayin ta na takara da sauran bangarorin duniya.

Bisa wannan aniya ne ma a ranar 10 ga watan Yunin shekarar bara, aka kaddamar da yarjejeniyar TFTA, wadda ke da nufin sake bunkasa tattalin arzikin nahiyar Afirka. Yarjejeniyar dai ta kunshi kungiyoyin bunkasa ci gaban nahiyar uku, wato SADC da EAC da kuma COMESA.

A ta bakin babban manajan kungiyar hadin gwiwar 'yan kasuwa da nahiyar Afirka, karkashin cibiyar ba da shawarwari ta "Deloitte Frontier" wadda ke Afirka ta kudu Dr. Martyn Davies, gudummawar Sin game da dunkulewar tattalin arzikin nahiyar Afirka na da matukar tasiri wajen samar da ci gaba na bai daya.

Ya ce, a gabar da ake dab da fara aiwatar da manufofin da za su baiwa nahiyar ta Afirka damar bunkasa masana'antun ta, manyan kudurorin ci gaba na kasar Sin guda 10 za su tabbatar da nasarar da ake fata, a bangaren samar da ci gaba mai fadi, da dorewa wanda kuma za ta kasance dama ta dora nahiyar kan turbar sauyi mai ma'ana.

Dr. Davies ya kara da cewa, shingaye da ake da su ta fuskar cinikayya, na zama tarnaki a fannin samar da ci gaban harkokin cinikayya a dukkanin fadin sassan nahiyar. Yayin da kuma tsare tsare na hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka, za su samar da damammaki na samar da guraben ayyukan yi, da kuma makoma mai haske ga nahiyar.

Tun daga shekara ta 2000 kawo yau, Sin na ci gaba da samar da tallafi tare da aiwatar da manufofin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, karkashin dandalin FOCAC na hadin gwiwar sassan biyu.

FOCAC ya kasance muhimmin dandali wanda tun kafa shi, ya zamo hanya da ke samarwa kasashen nahiyar Afirka gwaggwaban tallafi na miliyoyin daloli daga kasar Sin, domin bunkasa tattalin arzikin Afirka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China