in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron kolin kungiyar AU a birnin Kigali
2016-07-28 09:02:19 cri

A ranar Litinin 18 ga watan Yulin shekarar 2016 ne, aka rufe taron kolin kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU karo 27 a Kigali, babban birnin kasar Ruwanda, inda shugabannin kasashe daban daban na nahiyar suka tattauna batutuwa da dama kamar kalubalen da kasashen Afirka ke fuskanta a fannonin zaman lafiya da tsaro, da tara kudaden tafiyar da harkokin kungiyar, da kafa cibiyar shawo kan cututtuka a fadin nahiyar ta Afirka da dai sauransu.

Wani muhimmin batun da ba a saba ganin irinsa a lokacin taron kolin kungiyar ba shi ne, a wannan karon an jinkirta zaben sabon shugaban hukumar zartaswar kungiyar har zuwa taron kolin kungiyar karo na 28 da za a gudanar a farkon shekara mai zuwa bisa dalilin cewa, 'yan takarar da ke neman mukamin ba su samu isassun kuri'un da ake bukata ba.

Shugabar hukumar zartaswar kungiyar mai ci Nkosazana Dlamini Zuma ta bayyana cewa, wasu kasashen Afirka kamar Burkinafaso da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Madagaska suna sake gina kasashensu bayan da suka sha fama da hargitsi da katsalanda, hakan ya nuna cewa, ana iya sake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan faman da aka sha. Shi ma, shugaban kungiyar na karba karba, kuma shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya bayyana cewa, yanzu haka an zartas da kuduri game da kafa wata cibiyar shawo kan cututtuka a fadin Afirka, bisa shirin da aka tsara, ya zuwa shekarar 2030, za a shawo kan cutar Sida da tarin fukka, kuma za a kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro a fadin nahiyar ta Afirka.

Masu sharhi na ganin cewa, baya ga wadannan batutuwa, an kuma tattauna batun tabbatar da 'yancin mata, tsarin fasfo nahiyar na bai daya, samar da zaman lafiya da tsaro da makamantansu.

Masana na cewa. Kamata ya yi shugabannin nahiyar su mayar da hankali wajen kare muradun al'ummominsu, maimakon kokarin biyan bukatun kasashen da suka yi musu mulkin mallaka. Ta haka kadai za su cimma nasarar dukkan wasu manufofi da tanade-tanade da aka gabatar a tarukan kungiyar. (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China