in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AL: Kara hadin kai da kasar Sin nan gaba
2016-07-25 14:09:48 cri
Babban sakataren kungiyar kawancen kasashen Larabawa AL Mista Ahmed Ali Abul Gheit ya bayyana a jiya Lahadi cewa, AL tana yabawa shawarar da Sin ta bayar na "Ziri daya da hanya daya", kuma a ganinsa, bangarorin biyu za su kara hadin gwiwa tsakaninsu nan gaba.

Mista Gheit ya shedawa manema labaru kafin taron kolin kungiyar karo na 27 cewa, ban da dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin kasashen Larabawa da Sin, taron ministocin da aka yi ba da dadewa ba sun yi tasiri sosai ga hadin gwiwa tsakanin AL da Sin, a cikin wannan hali mai kyau Sin ta gabatar da shirin "Ziri daya da hanya daya", abin da zai sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin AL da Sin, kuma kasashen Larabawa na fatan zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu da kasar Sin nan gaba.

Game da taron kolin AL da za a kira, Mista Gheit ya ce, yanzu shugabannin kasashen Larabawa kimanin 10 sun tabbatar da halartar wannan taro. Ya kuma bayyana cewa, ana fatan a yayin taron za a zartas da kudurori da dama tare da gabatar da sanawar Nouakchott dake shafar harkokin siyasa, tattalin arziki, al'adu da sauransu, ta yadda za a tunkari kalubalolin da kasashen Larabawa ke fuskanta. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China