160725-Batun-neman-yancin-mata-a-yayin-taron-koli-na-AU-Kande.m4a
|
A cikin shirinmu na yau, za mu tattauna kan wani batun da ke jawo hankalin al'ummar Afirka, musamman ma matan da ke nahiyar Afirka, wato kokarin da ake yi na kare 'yancinsu a harkokin yau da kullum.
A ranar 17 ga wata ne, aka kaddamar da taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU karo na 27 a Kigali, babban birnin kasar Ruwanda, inda taron ya mayar da hankali ga kare hakkin mata, a matsayin wani muhimmin bangare na inganta ga ci gaban tattalin arziki, da siyasa, kana da rage yawan masu fama da kangin talauci a nahiyar Afirka. Masu sauraro, yanzu zan gabatar muku wasu daga cikin abubuwan da suka gudana a yayin taron, wadanda suka sheda mana cewa, lallai kokarin samarwa mata 'yanci ya haifar da babban tasiri ga matan Afirka da kuma zamantakewar al'ummar nahiyar daga dukkan fannoni.(Kande Gao)