160722-Kasar-Sin-na-kokarin-shigar-da-aikin-ba-da-hidimmar-jinya-ga-kowane-iyali-Lami.m4a
|
A lokacin da, ana tsammani da cewa, likitan iyali na da tsada sosai, amma a halin yanzu, hidimar jinya tana fara kaiwa ga kowane iyalin Sinawa. Ofishin majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gabatar da shawara game da raya aikin ba da hidima a gidaje, inda aka bayyana cewa, za a yi kokarin tabbatar da ba da hidimar jinya ga kowane iyalin Sin kafin shekarar 2020. Su wanene zasu zama likitocin iyali? Wane irin hidimomi ne da likitocin iyali za su samar? Kuma wa zai biya kudin hidimar? Ko akwai tsada? Bari mu ji cikakken labari.