in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda ake shagulgulan karamar Sallah a nan kasar Sin
2016-07-18 15:46:03 cri

A ranar Laraba 6 ga watan Yulin shekarar 2016 ne musulmi a sassa daban-dabab an duniya, ciki har da nan kasar Sin suka yi bikin karamar sallah ta wannan shekara, bayan shafe tsawon wata guda cur ana Azumin watan Ramadan wato daya daga cikin shika-shikan musuluncin nan guda biyar.

Kamar sauran kasashen musulmi na duniya haka ma a nan kasar Sin, musulmi sun yi tururuwa zuwa masallatai da ke wurare daban-daban a wannan rana karkashin tsauraran matakan tsaro don gudanar da sallah mai raka'a biyu suna sanye da sabbin tufafi cikin farin ciki da annashuwa.

Koda yake bayanai na nuna cewa, tun a ranar Talata 5 ga watan Yuli ne al'ummar musulumi a Jamhuriyar Nijar suka yi bikin karamar sallah bayan ganin jaririn watan Shawwal a wasu sassan kasar.

Sai dai ba kamar yadda aka saba hawan Daba ko Daushe na dawakai a lokutan sallah a kasashenmu na Afirka inda ake kade-kade da bushe-bushe a irin wannan rana, a nan lamarin ya sha bambam kamar yadda masu iya magana ke cewa, "Allah daya gari bambam". Sai dai su ma musulmi da ke nan kasar Sin kan yi irin nasu shagulgulan, baya ga ziyartar 'yan uwa da abokai da gaishe-gaishe da nau'o'in abinci da ake dafawa don murnar wannan rana.

Abu mai muhimmanci a nan kasar Sin shi ne yadda ake samar da matakan tsaro a ranakun sallar Azumi da Lahiya da ma sauran lokutan da musulmi ke gudanar da salloli a masallatai a duk fadin kasar.

Amma duk da irin bambancin da ke akwai, musulmi 'yan kasashen waje da ke nan Sin sun yi karamar sallah ta bana cikin farin ciki sai dai abin da ba za a rasa ba na kadaici, kuma masu salon magana na cewa, sallah bikin daya rana, ta tafi ta bar wawa da bashi.

Allah ya maimaita mana da alheri-Amin, sai kuma badi ga wanda ya ke da nisan kowa. (Ibrahim Yaya/Ahmed/Ada/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China