160718-wata-yariniya-dake-gudanar-da-ayyukan-sa-kai-a-jihar-Tibet-Bilkisu.m4a
|
Yankin Ali yana yammacin jihar Tibet ta kasar Sin mai ikon aiwatar da harkokinta, har ila yankin yana iyaka da kasashen Nepal, India da kuma yankin Kashmir. Yawan al'ummar yankin ya kai kimanin dubu 100, fadin muraba'in yankin ya wuce kilomita dubu 340. Har ila yana daya daga cikin yankuna marasa yawan jama'a a duniya. Tsawon yankin ya fi tsawon lebur din teku sama da mita 4300, yanayin wurin yana da sanyi sannan babu damshi a cikin iskar shakar wurin, Haka kuma yanayin wurin tamkar na Hamada, inda ake kwala zafi da rana a kuma sheka sanyi da dare. Duk da wadannan canje-canjen yanayin, akwai baki da zuwa yankin don gudanar da ayyukan sa-kai, ciki har da wata yarinya mai suna Deng Yujuan, wadda ta kammala karatunta a jami'a a shekarar da ta wuce. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani ne game da wannan yariniya.