in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi rajistar lambar shaidar mallakar fasahar murya ta farko a Sin
2016-07-15 10:45:00 cri

A ranar 14 ga watan Mayun bana, an ba da takardar shaidar mallakar fasahar murya kan "taken fara shirye-shiryen CRI" a hukumance, wannan lambar shaidar mallakar fasahar murya ta farko ce da aka yi rajista a kasar Sin, ana iya cewa, lamarin ya bude wani sabon shafi a fannin yin rajistar lambar shaidar mallakar fasahar murya a kasar.

An fara amfani da taken bude shirye-shiryen CRI ne tun daga ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1998, tsawon taken ya kai dakika 40. Sautin taken yana wakiltar yanayin da kasar Sin ke ciki a zamanin yau, yana nunawa al'ummomin kasa da kasa manyan sauye-sauyen da kasar Sin ta samu bayan da ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da kuma bude kofa ga kasashen waje, haka kuma ya nunawa al'ummomin kasa da kasa matsayin kasar Sin a duniya. Sautin kidan yana da karfi kuma yana da dadin ji, shi ya sa ya samu karbuwa sosai daga wajen masu sauraro.

Kazalika, sautin taken ya bayyana manufar CRI wato yin bayani kan kasar Sin ga kasashen duniya, da yin bayani kan kasashen duniya ga kasar Sin, da kuma yin bayani kan kasashen duniya ga kasashen duniya, tare kuma da kara karfafa fahimtar juna da zumunta dake tsakanin al'ummar kasar Sin da ta kasashen duniya baki baya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China