Mataimakin babban editan gidan rediyon CRI Ma Bohui da shugabar gidan telibijin ta MNB, madam Ts Ouyndari ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin kafofin watsa labaran biyu.
Yarjejeniyar ta tanadi cewa, bangarorin biyu za su yi hadin gwiwa a fannonin musayar shirye-shirye da gabatarwa, da zurfafa tsarin hadin gwiwa na gabatar da labarai dangane da muhimman batutuwa, da yin musayar ma'aikata da sauransu. Kuma yarjejeniyar ta jaddada cewa, bangarorin biyu za su yi ayyuka tare dangane da muhimman batutuwa da ayyukan tunawa na kasashen biyu, domin gabatar da labarai ta hanyoyi daban daban. Daddale yarjejeniyar zai taka muhimmiyar rawa wajen kara sada zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu da zurfafa dangantaka tsakanin Sin da Mongoliya.(Fatima)