160711-Gudu-na-kara-samun-karbuwa-tsakanin-mata-Sinawa-Kande.m4a
|
Ko kun san a yanzu haka adadin mata masu gudu sai karuwa yake yi a 'yan shekarun nan a daukacin fadin kasar Sin? A watan Maris din bara aka yi gasar farko na gudun yada-kanin-wani na mata a birnin Shenzhen, garin dake lardin Guandong a kudancin kasar Sin, abin da ya jawo hankalin mahalarta mata 3,000 daga gida da waje.
Daga baya kuma har ila yau a watan na Mayun bara an yi rabin tseren gudu a gabasin kasar Sin a birnin Shanghai. Wanda a nan kusan 'yan gudu 5,000 suka shiga gasar kuma kusan rabin su mata ne.
Bugu da kari, a watan Afrilu na bana, an yi gasa ta karo na biyu ta gudun yada-kanin wani na mata a birnin Shenzhen, wanda kuma ya jawo hankaluna mahalarta mata fiye da 3000. Amma idan aka kwatanta da gasar ta bara, to za a iya gano cewa, akwai bambanci sosai, wato wasu kungiyoyin mata sun sa hannu a cikin gasar, ciki har da kungiyar malamai mata, da ta likitoci mata, da ta lauyuka mata, da ta 'yan kasuwa mata da dai sauransu. Haka zakila ma, wasu mata sun shiga gasar ne tare da yaransu, wadanda a ganinsu, gudun ba ma kawai ya kasance wani wasan motsa jiki ba, hatta ma wata hanya ce wajen kyautata zamansu na yau da kullum. (Kande Gao)