160708-Shugaba-Xi-ya-yi-kira-da-a-kiyaye-burinsu-na-lokacin-farko-Lami.m4a
|
A ranar 1 ga wata, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin Xi Jinping ya ba da muhimmin jawabi a gun taron taya murnar cika shekaru 95 da kafa jam'iyyar JKS, inda ya waiwayi yunkurin kafa kasa da kuma neman samun bunkasuwa a cikin shekaru 95 da suka gabata, ya kuma bayyana cewa, kada 'yan jam'iyyar su manta da burinsu na shiga jam'iyya, sai dai su rika yin kokarin cimma burinsu, za su iya samu sakamako mai kyau wajen aiki. Wasu kwararru suna ganin cewa, shugaba Xi ya kalubalanci dukkan 'yan jam'iyya wajen tsayaya niyyarsu ta ba da hidimma ga jama'a da raya kasa ba tare da kasala ba.