in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba zai yiyu Sin ta amince da hukunci maras ma'anar doka ba kan batun tekun kudancin kasar
2016-07-07 10:57:07 cri

Kotun da aka kafa bisa bukatar kasar Philippines a Hague za ta yanke hukunci kan batun tekun kudancin kasar Sin a ranar 12 ga wata, yanzu dai sabon shugaban Philipines ya bayyana cewa, yana son yin tattaunawa da kasar Sin bayan yanke hukuncin, a game wannan, jiya Laraba kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a yayin taron manema labaran da aka saba yi cewa, kasar Sin ba za ta amince da hukuncin da za a yanke kan batun ba, kana kasar Sin ba za ta amince da ra'ayoyi ko matakan da za a dauka bisa tushen wannan hukuncin ba, kuma kasar Sin tana fatan sabuwar gwamnatin Philippines za ta yi kokari tare da kasar Sin, ta yi watsi da matakan kuskuren da tsohuwar gwamnatin kasar ta dauka domin warware rigingimun yadda ya kamata.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, sojojin ruwan kasar Sin suna gudanar da rawar daji a yankin tekun dake kusa da tsibiran Xisha, lamarin ya jawo hankalin al'ummomin kasashen duniya, bisa labarin da hukumar kula da harkar teku ta kasar Sin ta bayar, an ce, za a ci gaba da rawar daji har zuwa ranar 11 ga wata, wato rana daya kafin yanke hukuncin karshe kan batun tekun kudancin kasar Sin.

A ranar 4 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Vietnam ya bayyana cewa, rawar dajin da kasar Sin ke yi a yankin tekun kudancin kasar Sin ta keta hakkin mulkin kasarta, kuma ya bukaci kasar Sin da ta daina yin rawar daji. Game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a jiya cewa, rawar dajin da ake yi a yankin rawar daji ne da aka saba yi bisa shirin shekara shekara na sojojin ruwan kasar Sin, ana gudanar da aikin ne a yankin teku karkashin ikon mulkin kasar, ba shi da nasaba da wata kasa ta daban ko kadan. "Tsibiran Xisha yankin kasar Sin ne, babu wanda ya nuna shakku kan batun. Rawar dajin da ake gudanarwa aiki ne da aka saba yi bisa shirin shekara shekara na sojojin ruwan kasar Sin, bai shafar wata kasa ta daban, shi ya sa bai kamata ba sauran kasashe su nuna ra'ayoyinsu kan wannan."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, sojojin ruwan kasar Sin sun taba gudanar da rawar daji sau da dama a tekun kudancin kasar, misali, a watan Yulin shekarar 2015, kasar Sin ta taba yin rawar daji a yankin, a wancan lokaci ta tura jiragen ruwan yaki sama da 100 da jiragen saman yaki sama da goma, kana ta tura sojojin rokoki da sojojin samar da taimako. A shekarar 2014 da ta 2013, kasar Sin ta taba yin rawar daji a tekun kudancin kasar.

Darektan kwamitin kwararru a harkokin sadarwa na sojojin ruwan kasar Sin, Yin Zhuo ya yi nuni da cewa, makasudin da ya sa sojojin ruwan kasar Sin suke gudanar da rawar daji shi ne domin nuna wa al'ummomin kasa da kasa karfin kiyaye hakkin teku na kasar Sin. Yin Zhuo yana mai cewa, "Kasar Sin tana yin rawar dajin ne a yankin tekun kudancin kasar, lamarin ba shi da nasaba da lokacin da za a yanke hukuncin karshe kan batun tekun kudancin kasar, rawar daji ne bisa shirin kasar. A baya an ce, za a yanke hukunci kan batun a watan Mayun bana, daga baya a jinkirta hukuncin, amma mun tsara shirin ne kafin lokacin. Yin rawar daji a yankin tekun kudancin kasar Sin yana da dalilai na siyasa, mu ma haka muke, makasudinmu shi ne muna fatan nunawa duniya karfin sojojin kasar Sin, musamman ma sojojin ruwan kasar Sin wajen samar da tsaro ga hakkin teku da hakkin yankin kasarmu ta hanyar yin rawar daji. Muna son sanar da cewa, ba zai yiyu ba a canja matsayin kasar Sin ta hanyar amfani da karfin tuwo."

Yin Zhuo ya ci gaba da cewa, wasu manyan kasashen dake nesa da yankin suna da makarkashiyar matsin lamba ga kasar Sin da ta amince da hukuncin da za a yanke kan batun tekun kudancin kasar Sin, hakan ba zai yiwu ba. Yin Zhuo yana mai cewa, "Idan wasu manyan kasashe suna son tsoma baki a cikin harkokin dake shafar batun tekun kudancin kasar Sin, to wajibi ne su samar da dalilan da suke da ma'anar doka, dokar kasa da kasa ita ma ba za ta amince da kasashen dake nesa da yankin su tilastawa kasar Sin da ta amince da irin wannan hukunci maras ma'anar doka ba. Ko shakka babu wadannan manyan kasashe ba za su cimma burinsu ba."

Ya kamata kasashen dake nesa da yankin su kara yin kokari domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya shiyya. A halin da ake ciki, asusun zaman lafiyar kasa da kasa na Carnegie yana gudanar da taron tattaunawa kan batun tekun kudancin kasar Sin a birnin Washington na kasar Amurka, masanan Sin da Amurka sun samu ra'ayi daya kan batun, inda suka bayyana cewa, karar da Philipines ta gabatar kan batun tekun kudancin kasar Sin ba ta bisa doka, ita ma tana da makarkashiyar siyasa maras ma'ana, a don haka, babu dalilin da zai sa kasar Sin ta amince kuma ta karbi hukuncin da za a yanke.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China