in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fitar da Iceland daga gasar EURO 2016
2016-07-07 17:05:54 cri

An fitar da kasar Iceland daga gasar EURO 2016 sakamakon kashin da ta sha a hannun kasar Faransa a wasan da suka buga.

Duk da cewa an fitar da kasar daga gasar, amma ta ba 'yan kallo da 'yan wasan daga sauran kasashe mamaki sosai a wannan karo. Kasar ta Iceland dai ta buga gasanni 5, inda ta zura kwallaye 8, wanda ya burge jama'a sosai.

Yawan al'ummar kasar Iceland dai dubu 330 ne kawai, don haka kasar ta zama kasa mai yawan mutanenta ya fi karanta a tarihi da ke halartar gasar ta Euro ta bana, kana a wannan karo, 'yan wasan kasar sun kafa bajimta, inda suka kai wasan kusa da na karshe a gasar ta wannan karo.

Duk da kashin da 'yan wasan suka sha a hannun kasar Faransa a wasan da suka buga, masu sha'awar kwallon kafa a kasar sun yaba da rawar da 'yan wasan suka taka, kana 'yan wasan kungiyar kasar Faransa su ma sun yabawa 'yan wasan kasar ta Iceland.

Bayan da aka fitar da Iceland daga gasar EURO ta bana, ana fatan za su kai ga shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018.

Tawagar kwallon kafa ta Faransa ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da ta doke Iceland da ci 5-2 a karawar da suka yi a filin wasan kasar ta Faransa a ranar Lahadi.

Faransa ta fara cin kwallo ta hannun Olivier Giroud, sai Paul Pogba ya kara ta biyu, Dimitri Payet ne ya ci ta uku, sannan Antoine Griezman ya ci kwallo ta hudu daf da za a je hutun rabin loaci.

Bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci ne Iceland ta samu nasarar zara kwallo ta hannun Kolbeinn Sigthorsson da kuma wadda Birkir Bjarnason ya ci daf da za a tashi daga karawar, kafin nan Faransa ta ci kwallo na biyar ta hannun Olivier Giroud.

I zuwa yanzu Antoine Griezman ne ke kan gaba a matsayin wanda ya fi cin kwwallaye a gasar, Inda ya zura hudu a raga a wasannin.

Da wannan sakamakon Faransa mai masaukin baki, za ta kara da Jamus a wasan daf da karshe a ranar Alhamis a Marseille.

Jamus ta kai wasan daf da karshe ne a gasar, bayan da ta fitar da Italy a bugun fenariti da ci 6-5, bayan da suka tashi wasa kunnen doki 1-1.

Iceland, kasa mafi kankanta ta kafa tarihi na karawa da manyan kasashe a wasannin, bayan da suka nuna bajinta mintuna 84 da fara wasan yayin da dan wasan kasar Birkir Bjarnason ya fara zura kwallo. Sai dai galabar da kasar Faransa ta yi kan kasar ta Iceland ya sa an fidda kasar daga wasan.(Zainab+Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China