in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta cika shekaru 95 da kafuwa
2016-07-06 18:35:30 cri

A ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2016 ne jam'iyyar kwaminis ta Sin ta cika shekaru 95 da kafuwa. A wannan rana da safe, kwamitin tsakiya na JKS ya kira taro a babban dakin taron jama'ar kasar Sin dake nan birnin Beijing, domin murnar wannan rana.

Har ila a wannan ranar ce aka ba da lambobin yabo ga fitattun mambobin jam'iyyar daga wurare daban daban na kasar Sin da kuma sassan JKS da suka taka rawar gani. Babban sakataren JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a jawabin da ya gabatar cewa, ya kamata daukacin 'ya'yan jam'iyyar su ci gaba da yin kokarin gwagwarmayar aiki kamar yadda suka yi a farkon lokacin kafa jam'iyyar, tare kuma da karfafa niyyarsu ta bauta wa al'umma.,

A shekarar 1921 ne aka kafa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, lokacin da jama'ar Sin ke cikin wani mawuyacin hali tare kuma da fuskantar matsaloli masu yawa, a lokacin da ma'aikata suka yi yunkurin juyin juya hali ta hanyar yin amfani da ra'ayin Markisanci da Lenin.

Tun lokacin ne jam'iyyar kwaminis ta Sin ta jagoranci jama'ar Sin wajen kafa sabuwar gwamnatin Sin, sa'an nan jam'iyyar ta bullo da wani tsarin gurguzu na musamman mai siga irin ta kasar Sin, daga bisani kuma, ta aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a cikin shekaru 30 din da suka gabata, har ma kasar Sin ta bunkasa sosai daga matsayin kasa mai tasowa mafi girma a duniya zuwa matsayin kasar ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Bugu da kari, shugaba Xi ya bayyana cewa, ra'ayin Markisanci da Lenin sun kasance jagora ga JKS,a don haka dole ne a ci gaba da amfani da su wajen daidaita batutuwa da tinkarar kalubale, kana ya kamata a hada wannan ra'ayi tare da ayyukan da ake gudanarwa a yunkurin bunkasa zaman al'ummar Sin.

Masana na bayyana cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin ta samu sakamako mai kyau a hulda da harkokin kasashen waje, ba ma kawai ta sada zumunci tare da karin kasashen duniya ba, har ma ta sauke nauyin dake bisa wuyanta a fannin harkokin kasa da kasa yadda ya kamata, baya ga matakan ba sani ba sabo na yaki da cin hanci da karbar rashawa. (Ahmed/ Ada/Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China