Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan cikin sakon taya murna da ya aikawa sabon shugaban, ya kuma bayyana cewa, a shirye yake ya yi aiki da shi ta yadda za a inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Xi ya bayyana a cikin sanarwar cewa, kasashen Sin da Philippines makwabtan juna ne da bai kamata su yi watsi da juna ba. Har ila yau, kasashe ne da suka gaji tarihin kyakkyawar makwabtaka da abokantaka na dubban shekaru, a saboda haka wajibi ne a bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.(Ibrahim)