Shugabannin sun bayyana hakan ne lokacin da suke jawabi a taron tattauna batutuwan samar da zaman lafiya da tsaro da ke damun kasashen nasu, wanda ya gudana a Oyo mai nisan kilomita 400 daga Brazzaville.
Har ila yau shugabannin sun bayyana cewa, suna goyon bayan yarjejeniyar Ezulwini, wata matsaya da aka cimma game da huldar kasa da kasa da yin gyare-gyare a MDD,wadda ta samu amincewar kungiyar tarayyar Afirka.
Ita dai wannan yarjejeniya tana kira ne da a kara wakilicin kasashen Afirka a kwamitin sulhu bisa tsarin demokuradiya, ta yadda nahiyar Afirka kamar sauran shiyoyin duniya za ta samu wakilci.
Yarjejeniyar Ezulwini tana ganin cewa, kamata ya yi nahiyar Afirka ta samu kujerun din-din-din a kwamitin sulhu na MDD da wasu kujeru guda biyu da bana din-din-din ba a kwamitin sulhun.(Ibrahim)