Duncan ya wanda ya yi wannan kiran jiya lokacin da ya ke jawabi a ofishin kungiyar ECOWAS da ke birnin Abidjan, ya bayyana cewa, muddin kasashe mambobin kungiyar suka kara yin hadin gwiwa, hakan zai taimakaa wajen magance kalubalen tsaro da shiyyar ta ke fuskanta.
Alkaluma na nuna cewa, a shekarar da ta gabata an samu karuwar hare-haren ta'addanci da ake kaiwa masu yawon shakatawa ko wuraren da baki 'yan kasashen waje suke zuwa a kasashen Afirka.(Ibrahim)