in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kaddamar da sabon samfurin na'urar harba roket
2016-06-26 13:12:54 cri

A jiya Asabar kasar Sin ta harba sabon samfurin roket na daukar kaya nau'in Long March-7 daga sabuwar cibiyar harba na'urori zuwa sararin samaniya mallakar kasar, wadda ke yankin Wenchang, a lardin Hainan.

Wang Hongyao, shi ne mataimakin babban kwamandan shirin, ya bayyana cewar aikin ya samu nasara ne bayan 'yan mintuna kadan da harba na'urar.

Ita dai samfurin roket ta Long March-7 matsakaiciya ce, tana da bangarori biyu ta yadda zata iya daukar kaya sama da ton 13.5 zuwa sararin samaniya. Kwararru sun bayyana cewar roket zai iya kansancewa a matsayin babbar na'urar daukar kaya da kasar Sin zata dinga amfani da ita a nan gaba wajen gudanar da ayyuka a sararin samaniya.

Aikin harba roket din na ranar Asabar, shine irinsa na farko da aka gudanar a yankin na Wenchang, kuma shine na 230 cikin jerin rokokin nau'in Long March da kasar Sin ta harba zuwa sararin samaniya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China