160624-ana-fatan-kafofin-watsa-labaran-afirka-su-nace-ga-kaidar-adalci-kan-batun--tekun-kudancin-sin.m4a
|
Jiya Alhamis, mataimakin ministan yada manufar kasar Sin kuma daraktan ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin Jiang Jianguo ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana fatan kafofin watsa labarai na kasashen Afirka za su nace ga ka'idar yin adalci yayin da suke watsa labarai kan batun da ya shafi tekun kudancin kasar Sin, da haka za su iya yin bayani kan asalin batun tekun kudancin ga al'ummar kasashen Afirka, da ma al'ummomin duniya baki daya.
Wannan rana, mataimakin ministan yada manufar kasar Sin kuma daraktan ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin Jiang Jianguo ya halarci dandalin ci gaban shirye-shiryen talebijin da aka tsara ta hanyar yin amfani da fasahar zamani na kasashen Afirka karo na 6 da aka shirya a nan birnin Beijing, kuma ya gabatar da jawabi a yayin dandalin, inda ya yi bayani kan manufar da gwamnatin kasar Sin take dauka kan batun tekun kudancin kasar da kuma matakan da za ta dauka kan batun ga ministocin watsa labarai da shugabannin kafofin watsa labarai na kasashe daban daban.
Jiang Jianguo ya bayyana cewa, kafin shekarun 1970, tsibirrai dake tekun kudancin kasar Sin suna karkashin ikon kasar Sin ne, kuma babu wanda ya nuna shakku kan wannan batun, kana babu wata kasa ko guda da ta kai kalubale kan ikon mallakar kasar Sin dake tekun kudancin kasar, kuma babu kasa da ta sanar da cewa, tekun kudancin kasar Sin yana karkashin mallakinta. Amma daga bisani, sakamakon albarkatu da arziki dake makare a wurin, tun daga shekarun 1970, wasu kasashen dake gabar tekun suka fara mamaye wasu tsibirorin Nansha na kasar Sin dake tekun kudancin kasar Sin daya bayan daya, kana kasar Philipines da wasu kasashe suka fara yin makarkashiyar musanta ikon mallakar tsibiran Nansha na kasar Sin bisa aron baki na ikon gudanar da harkokin teku.
Kan batun, Jiang Jianguo ya bayyana cewa, a wancan lokaci, kasar Sin tana da ikon karfin hana a kwace yankinta, amma ba ta dauki matakai ba, sai ta yi hakuri, yanzu kuma, lokaci ya yi da kasar Sin ba za ta ci gaba da yin hakuri ba, saboda lamarin yana shafar ikon mulkin kasar Sin, wajibi ne gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai kansa.
Jiang Jianguo ya jaddada cewa, har kullum gwamnatin kasar Sin ta nace ga ka'idarta ta warware rigingimun kan ikon mallakar yankin kasa ta hanyar yin shawarwari karkashin dokokin kasa da kasa da kuma bisa tushen nuna biyayya ga tarihi na gaskiya.
Tun daga shekarun 1960, gwamnatin kasar Sin ta warware sabani kan ikon mallakar yankin kasa dake tsakaninta da kasashe 12 daga cikin kasashe 14 masu makwabtaka da ita ta hanyar yin shawarwari cikin ruwan sanyi. Ana iya cewa, wannan shi ne sakamakon da kasar Sin ta samu wajen harkokin waje, kuma hakan ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana aiwatar da manufofinta na harkokin waje yadda ya kamata, kuma hakan ya gaskanta cewa, kasar Sin tana kokarin aiwatar da kuma kiyaye dokokin kasa da kasa.
A cikin shekaru sama da goma da suka gabata, sassa daban daban da abin ya shafa sun bar sabanin sun yi hadin gwiwa tsakaninsu kuma sun yi kokari domin tafiyar da harkoki a tekun kudancin kasar Sin lami lafiya.
Jiang Jianguo ya ci gaba cewa, kasar Philipines ta shigar da kara a kotun yanke hukunci ba zato ba tsamani, sannan ba ta ma sanar da kasar Sin lamarin ba, kana ba ta ma nemi amincewar kasar Sin kafin daukar wannan mataki ba. Shi ya sa ana iya cewa, matakin nan da Philipines ta dauka bisa gefe guda wasa ne maras kai, ba shi da amfani ko kadan wajen doka, ba zai yiyu ba a warware matsalar, zai tada tarzoma ne kawai, Philipines za ta dauki darasi daga wannan.
Jiang Jianguo ya kara da cewa, game da iyakar kasa kan teku, yarjejeniyar dokar teku ta MDD ta tanadi a kashi na 298 cewa, kasar da ta daddale yarjejeniyar tana da ikon nuna kiyayya, kuma a shekarar 2006, kasar Sin ta sanar da cewa, ba za ta amince da wasu matakan da za a dauka domin warware sabani, wanda a ciki ya hada da matakin yanke hukunci. Ban da kasar Sin, sauran kasashen duniya sama da 30 sun taba daukar irin wannan mataki.
Jiang Jianguo ya ce, kan batun tekun kudancin kasar Sin, wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma suna watsa labarai irin yadda suke so, har ma ba su bayar da labarai na gaskiya, kasar Sin tana fatan kafofin watsa labarai na kasashen Afirka za su kara mai da hankali kan batun, kuma su watsa labarai bisa ka'idar adalci, da haka za su yi bayani kan asalin batun ga al'ummar kasashen Afirka, da ma al'ummomin kasashen duniya baki daya.(Jamila)