in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya yi jawabi a Uzbekistan
2016-06-23 13:15:53 cri


Jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ci gaba da gudanar da ziyara aikinsa a kasar Uzbekistan. Wannan rana da yamma, shugaba Xi ya bayar da wani jawabi a majalisar dokokin kasar dake Toshkent, fadar mulkin kasar ta Uzbekistan, wannan ne jawabi guda daya kadai da ya yi a fili a yayin ziyarar aikin da yake yi a wannan karo.

A cikin jawabin da ya bayar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, a cikin shekaru uku da suka gabata, an samu babban sakamako a fannoni daban daban yayin da ake kokarin aiwatar da shirin "ziri daya da hanya daya", gwamnatin kasar Sin tana son ci gaba da yin kokari tare da sassan da abin ya shafa domin ciyar da shirin gaba yadda ya kamata.

Yan majalisar dattijai da 'yan majalisar dokoki da manyan jami'an gwamnatin kasar ta Uzbekistan sama da 200 sun saurari jawabin da shugaba Xi Jinping ya bayar. A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya mai da hankali sosai kan shirin "ziri daya da hanya daya", inda ya bayyana cewa, dalilin da ya sa ya kai ziyara a wadannan kasashe uku na Turai da Asiya wato Serbia da Poland da kuma Uzbekistan shi ne domin kara sai kaimi kan wannan shirin.

A shekarar 2013, shugaba Xi ya gabatar da shawarwari game da shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21 yayin da yake kai ziyara a kasashen dake tsakiyar Asiya da kudancin Asiya. Tun daga wancan lokaci, kawo yanzu, shekaru uku suka wuce ke nan, shawarar game da shirin "ziri daya da hanya daya" ta samu karbuwa daga wajen kasashen da abin ya shafa, kuma shirin ya samu babban ci gaba yadda ya kamata. A halin da ake ciki yanzu, gaba daya kasashe da kuniyoyin kasa da kasa sama da 70 sun shiga shirin, kuma kasar Sin ta daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa dake tsakaninta da kasashe fiye da 30. Shugaba Xi ya bayyana cewa, "Kasar Sin ta daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa wajen samar da kayayyaki tare da kasashe 20, kuma tana gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninta da kasashe 17 da abin ya shafa domin gina yankunan hadin gwiwa a kasashen ketare da yawansu ya kai 46, gaba daya adadin jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba kan ayyukan ya kai dalar Amurka biliyan 14, har sun samar da guraben aikin yi dubu 60 ga masu bukata. Kana bankin zuba jari kan manyan kayayyakin more rayuwar al'umma na Asiya ya fara aiki a hukumance, kasashe 57 suna aiki cikin hadin gwiwa a bankin. Ban da haka, an kafa asusun hanyar siliki da asusun hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin Sin da kasashen Turai da Asiya lami lafiya. Yanzu dai ana iya cewa, an riga an kammala aikin shirin ziri daya da hanya daya a matakin farko lami lafiya, za a ci gaba da sanya kokari domin ciyar da shirin gaba yadda ya kamata."

Game da shirin da za a tsara a nan gaba, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu, ya kamata a kafa wani tsarin hadin gwiwa na moriyar juna na shirin ziri daya da hanya daya. Yana mai cewa, "Kasar Sin tana son kara zurfafa hadin gwiwa dake tsakaninta da kasashen da shirin ya shafa bisa ka'idar yin shawarwari da moriyar juna, da haka za a kafa wani sabon tsarin yin hadin gwiwa kan shirin ziri daya da hanya daya."

Shugaba Xi ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana son yin kokari da wadannan kasashe domin kara kyautata manyan kayayyakin more rayuwar al'umma da kuma kara zurfafa hadin gwiwa a fannonin samar da kayayyaki da harkar kudi da kuma al'adu. Shugaba Xi ya bayyana cewa, "Muna son kara zurfafa hadin gwiwa wajen kiyaye muhalli yayin da muke aiwatar da shirin ziri daya da hanya daya, kana muna son yin hadin gwiwa wajen kiwon lafiya, da horas da kwararru da kuma harkar samar da tsaro, ta yadda za a aiwatar da shirin cikin kwanciyar hankali."

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashen dake tsakiyar Asiya domin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin da kasashen tsakiyar Asiya da kuma yammacin Asiya.

Shugaban Uzbekistan Islam Karimov ya bayyana cewa, kasarsa tana son kara zurfafa zumuncin dake tsakaninta da kasar Sin, kuma tana son kara yin hadin gwiwa da kasar Sin domin samun moriyar juna. Yana mai cewa, "Yau, mun daddale takardun hadin gwiwa da dama, wadannan takardun za su kara ciyar da huldarmu gaba yadda ya kamata. Ina fatan kowa da kowa za su fahimci babbar ma'anar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Uzbekistan, ina fatan al'ummar kasarmu za su darajanta hadin gwiwar dake tsakaninmu."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China