A cikin wata sanarwa da aka fitar kan wannan lamari, gwamnatin Congo ta jaddada cewa harin da har yanzu ba a tantance wadanda suka aikata shi ba, ya janyo gobara a wani bangaren ginin jakadancin da kuma lalata kayayyaki da ake cigaba da kiyastawa.
Gwamnatin Congo na yin allawadai da wannan harin ta'addanci da babbar murya tare da yin kira kuma ga hukumomin Faransa da su gudanar da bincike domin tantance masu hannu kan wannan lamari tare da gurfanar dasu gaba kotu, in ji sanarwar. (Maman Ada)