in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da dandalin hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaran Sin da Afirka karo na 3 a Beijing
2016-06-22 12:58:17 cri

Jiya Talata, an kaddamar da dandalin hadin gwiwa dake tsakanin kafofin watsa labaran kasar Sin da kasashen Afirka karo na 3 a nan birnin Beijing. Wakilan da suka zo daga kafofin watsa labaran kasar Sin da kasashen Afirka 46 suke halartar dandalin. Yayin dandalin, za a tattauna batutuwan da suke shafar cudanyar manufofi kan rediyo da talabijin da fina-finai na Sin da Afirka, da hadin gwiwar kafofin watsa labaran Sin da Afirka da kara kyautata aikin, da ci gaban rediyo da talebijin ta hanyar yin amfani da fasahar zamani da dai sauransu.

An bude dandalin hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaran Sin da Afirka bisa tsarin dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, shi ma babban taron manyan jami'an kafofin watsa labarai dake tsakanin gwamnatocin kasashen Sin da Afirka ne. An gudanar da dandalin karo na farko ne a shekarar 2012, na karo na biyu kuma, an gudanar da shi a shekarar 2014.

Yayin wannan dandalin da ake gudana a nan birnin Beijing, wakilai kusan 250 wadanda suka hada da ministocin gwamnatoci 26 da mataimakan ministan 14 da shugabannin kafofin watsa labarai wajen 80 za su tattauna batutuwan da suka fi jawo hankalin sassan biyu a yayin da suke kokarin yin hadin gwiwa a fannin. Wakilan kasar Sin 70 da suke halartar dandalin sun fito ne daga hukumomin gwamnati da muhimman kafofin watsa labarai da wasu kamfanonin samar da hidimar fasaha.

Shugaban hukumar kula da watsa labarai da dab'i da rediyo da talebijin ta kasar Sin Cai Fuchao ya bayyana cewa, yayin da ake gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin kafofin watsa labarai na Sin da Afirka, kamata ya yi a mai da hankali kan fannoni da dama. Yana mai cewa, "Ya kamata kafofin watsa labaran Sin da Afirka su kara fahimtar jama'ar Sin da Afiirka, musamman ma matasa game da zumuncin dake tsakanin sassan biyu, ta yadda za a ciyar da shi zuriya zuwa zuriya. Kana muna son ci gaba da samar da taimako ga kasashen Afirka a fannin bunkasa kafofin watsa labaran kasashen Afirka ta hanyar yin amfani da fasahar zamani, misali, gudanar da harkokin kafofin watsa labarai da hidimar fasaha da horas da ma'aikata da tsara shirye-shirye da dai sauransu. Ban da haka kuma, muna sa ran za mu yi kokari tare domin daga matsayin hadin gwiwar rediyon da talebijin dake tsakaninmu, tare kuma da yin hadin gwiwa wajen gudanar da harkokin kafofin watsa labaran sassan biyu, da haka za a daga matsayin rediyo da talebijin Sin da Afirka yadda ya kamata."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, ana gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin kafofin watsa labaran Sin da Afirka lami lafiya, misali, a fannonin musayar labarai da horaswar da ma'aikata da kyautata fasahar na'ura. Bisa alkaluman da aka samu, an ce, ana watsa wasan kwaikwayon kasar Sin a kasashen Afirka sama da 40, a sa'i daya kuma, shirye-shiryen da aka tsara kan abubuwan dake shafar kasashen Afirka su ma sun shiga gidan rediyo da talabijin na kasar Sin, har sun samu karbuwa sosai daga wajen Sinawa. A cikin shekaru 4 da suka gabata, shirye-shiryen da gidan talebijin tsakiyar kasar Sin wato CCTV ya watsa kan nahiyar Afirka sun kai tsawon awoyi sama da 4600, gidan rediyon kasar Sin wato CRI namu kuwa shi ma yana watsa labarai da harsuna da dama a kasashen Afirka. Kana gidan talebijin tsakiya na kasar Sin reshensa na Afirka da babbar tashar Afirka ta gidan rediyon kasar Sin suna watsa labaran Afirka dumi dumi ga kasar Sin da kasashen duniya baki daya.

A yayin taron kolin Johnnesburg na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a karshen shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, ya kamata a yi kokari domin kara karfafa hadin gwiwa da cudanya tsakanin kafofin watsa labaran sassan biyu.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Chao yana mai cewa, "An kaddamar da aikin cibiyar cudanyar kafofin watsa labaran Sin da Afirka ne a shekarar 2014, kawo yanzu, 'yan jarida wajen 50 na kasashen Afiirka sun zo nan kasar Sin domin kara saninsu, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da shirya kos na kara wa juna sani ga jami'an watsa labarai da 'yan jarida, da haka za a horas da ma'aikatan watsa labarai 1000 ga kasashen Afirka ko wace shekara."

Mahalarta dandalin da suka zo daga Afirka su ma suna fatan za a kara karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasashensu da Sin. Daraktan ofishin gwamnatin Afirka ta Kudu Donald Liphoko ya ce, "Kafofin watsa labaran kasashen Afirka na kokarin yin amfani da fasahar zamani wajen aiki, mun samu damar koyi da sakamakon da aka samu a wajen dandalin."

Yanzu wasu kafofin watsa labaran kasashen yamma suna kawo suka ga huldar dake tsakanin Sin da Afirka, kan wannan, mataimakin shugaban kungiyar tarayyar Afirka Eratus Mwensha ya jaddada cewa, wajibi ne a kara watsa labarai na sahihanci da gaskiya ga al'ummomi a fadin duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China