in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kafofin yada labarai na Sin da Afirka
2016-06-21 19:38:01 cri

A yau Talata, aka bude taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kafofin yada labarai na Sin da Afirka karo na uku a nan birnin Beijing, taron da ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga kasashen Afirka 46 da kuma kasar Sin.

Abubuwan da aka tattauna a gun taron, sun hada da manufofin da suka shafi rediyo da telebijin da kuma fina-finai da hadin gwiwar kafofin yada labarai a tsakanin sassan biyu da kuma fasahohin rediyo da telebijin na zamani da ci gaban kafofin yada labarai na zamani. Wakilan kasashen Chadi da Angola da Nijer da Uganda da kuma Tanzania sun bayyana manufofin kasashensu ta fannin kafofin yada labarai da kuma yanayin ci gaban kafofin yada labarai a kasashen.

A yayin taron, Sin da Afirka sun daddale takardun fahimtar juna 15 da suka shafi hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu, sa'an nan, an bayar da sanarwar bayan taron, wadda ta jaddada cewa, ya kamata a ba wa kafofin yada labarai na sassan biyu kwarin gwiwar yin musaya a tsakaninsu, domin kara taimakawa ci gaban huldar hadin gwiwa da abokantaka a tsakanin Sin da Afirka.

Taron wani bangare ne na taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka(FOCAC), kana babban taro ne da gwamnatocin kasashen Sin da Afirka suka shirya ta fuskar kafofin yada labarai. An taba gudanar da taron a shekarar 2012 da kuma ta 2014. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China