in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya ziyarci kamfanin narke karafa na Smederevo dake Serbia
2016-06-20 13:07:46 cri

Birnin Smederevo yana da tazarar kilomita 40 daga birnin Belgrade, babban birnin kasar Serbia, shi ma shahararren birni ne na kasar ta Serbia wanda ke da dogon tarihi. Jiya Lahadi da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin domin ziyarci kamfanin narke karafa na Smederevo, reshen kamfani na rukunin Hegang na kasar Sin. Yayin ziyararsa, shugaba Xi ya je dakin cin abinci tare da shugabannin kasar Serbia domin yin hira da ma'aikatan kamfanin, inda ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana sa ran za ta ci gaba da yin hadin gwiwa dake tsakaninta da kasar Serbia domin morewa jama'ar kasashen biyu.

An kafa kamfanin narke karafa na Smederevo ne a shekarar 1913, shi ya sa kamfanin yake da tarihi mai tsawon shekaru sama da dari daya, kamfanin narke karafen shi kadai ne ke karkashin mallakin gwamnatin kasar ta Serbia. A watan Aflilun bana, rukunin narke karafa na Hegang na lardin Hebei na kasar Sin ya sayi kamfanin da kudin Euro miliyan 46 domin ceto kamfanin daga mawuyacin halin durkushewa da ya shiga, har ya sake samun farfafowa. Yanzu dai, kamfanin wanda kasar Sin ta zuba jari a cikinsa ya samar da guraben aikin yi ga ma'aikatan kasar sama da dubu biyar, kana kamfanin na Smederevo ya kara samun karfin narke karafa har zai iya kasancewa kamfani mafi karfi a kasuwannin kasashen Turai.

Kan wannan batu, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, kamfanonin kasashen nan biyu wato Sin da Serbia suna gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu yadda ya kamata, hakan ya bude wani sabon shafi wajen hadin gwiwar samar da kayayyaki dake tsakanin kasashen biyu, shi ma ya nuna mana cewa, sassan biyu suna da niyyar kara zurfafa gyare-gyare, tare kuma da samun moriyar juna. Shugaba Xi yana mai cewa, "Na yi imanin cewa, muddin dai sassan biyu suka yi hadin gwiwa yadda ya kamata, za a samu sakamakon da ake zato, kamfanin narke karafa na Smederevo shi ma haka yake, ko shakka babu zai sake samun ci gaba yadda ya kamata, a sa'i daya kuma, zai kara samar da guraben aikin yi ga 'yan kasar, tare kuma da kara kyautata ingancin zaman rayuwar jama'ar dake wurin, a takaice dai, ana iya cewa, za a ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin Serbia lami lafiya, har kamfanin zai kasance abin koyi ga sauran kasashen dake tsakiya da kuma gabashin Turai, yayin da suke gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu da kasar Sin."

Kamfanin Smederevo da rukunin Hegang na kasar Sin ya saya a kasar ta Serbia, ya kasance kamfani na farko da kasar Sin ta saya a yankin tsakiya da gabashin Turai. Shugaban kasar Serbia ya bayyana cewa, kamfanin narke karafa na Smederevo, ya taba gamuwa da matsala yayin da yake kokarin samun bunkasuwa, yanzu dai yana samun haske yayin da yake yin hadin gwiwa da kasar Sin, wannan aikin hadin gwiwa ya samar da wata sabuwar dama ga kasashen Sin da Serbia yayin da suke yin hadin gwiwa. Shugaban kasar Serbia Tomislav Nikolic ya bayyana cewa, "Kasar ta Serbia tana da karfin samar da kayayyaki, al'ummar kasar suna da hikima da kuma kwazo, kana kasar tana da yanayin zuba jari mai inganci, ko shakka babu Serbia za ta iya samar da dama ga kasar Sin da ta shiga kasuwar kasashen Turai. Yanzu dai mun gano cewa, yana da muhimmanci sosai gare mu mu yi hadin gwiwar sada zumunta, nan gaba za mu sa kaimi kan ci gaban dangantakarmu."

Daga baya, shugabannin kasashen biyu sun je kamfanin Smederevo tare domin yin ziyara. Shugaba Xi Jinping ya duba kayayyakin karafun da aka narka, kana ya tambayi ma'aikatan kamfanin abubuwan da suke shafar fasahar narka karafa. Kazalika, shugaba Xi Jinping ya je dakin cin abinci karkashin rakiyar shugabannin Serbia. A dakin cin abinci, shugaba Xi ya tambayi ma'aikatan dake cin abinci a can wasu tambayoyi, kuma ya kara karfafa zuciyarsu da su kara yin kokari kan aiki. Yayin da yake yin hira da ma'aikatan kasar Sin dake aiki a kamfanin, ya jaddada cewa, "Da farko dai, ya kamata mu yi huldar aminci da ma'aikatan wurin, wannan shi ma wani abu ne da Sinawa ke mai da hankali kansa, an ce, aminci ya fi kome muhimmanci, in ba haka ba, ba zai yiyu a yi nasara ba, daga baya kuma, sai mu yi kokari domin samun moriyar juna ta hanyar yin hadin gwiwa, wannan dai ita ce ka'idar da ya kamata mu nace mata yayin da muke yin hadin gwiwa a tsakaninmu da sauran kasashen duniya."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China