in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan New Zealand: kasar Sin na da imani wajen yin gyare-gyare bisa hakikanin halin da take ciki
2016-06-19 12:46:56 cri
A jiya da rana, Asabar firaminista John Key na kasar New Zealand, ya fada cewar shugabannin kasar Sin suna da imani sosai wajen yin gyare-gyare bisa hakikanin halin da kasar Sin ke ciki a lokacin da ake kokarin canja salon bunkasa tattalin arzikinta.

John Key ya furta hakan ne a lokacin da yake halartar liyafar da kungiyar 'yan kasuwa na kasar Sin dake New Zealand ta shirya.

Sannan ya yi amana cewar hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da bunkasa a nan gaba.

Mr. John Key ya bayyana cewa, a lokacin da take sa kaimi wajen kirkiro sabbin fasahohin zamani, kasar Sin tana kokarin mayar da hankalinta ne wajen bunkasa tattalin arziki da ba da hidima, kuma tana kokarin bunkasa kasuwannin cikin gida maimakon fitar da kayayyaki kawai don bunkasa tattalin arziki.

Game da shakkar da kafofin watsa labaru na wurin suka yi kan matakan hada-hadar kamfanonin kasar da na kasar Sin suka dauka a kasar New Zealand, John Key ya bayyana cewa, yunkurin hana shigar da jarin waje ba wani sabon batu ba, hakikanin dalilin da ya sa aka ji tsoron jarin waje shi ne ba a fahimci hakikanin ma'anar karfin jari ba. A hakika dai kasar Sin ba ta kasance kasa ce mafi girma ba wajen zuba jari a kasar New Zealand. A bangare guda kuma, kamfanonin kasar Sin suna samar da guraben aikin yi, suna sayen kayayyaki a kasar New Zealand, har ma suna bayar da gudummawa ga bunkasar tattalin arzikin kasar New Zealand, in ji John Key. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China