160622-Takaddama-tsakanin-NDA-da-mahukunta-Najeriya-Sanusi.m4a
|
A kwanakin baya ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana aniyarta na tattaunawa da sabbin mayakan kungiyar tsagerun yankin Niger Delta mai arzikin mai da ke kudancin kasar wato "Niger Delta Avengers" ko NDA a takaice.
Wannan kungiya dai tana ta kaddamar da hare-hare kan kamfanonin hakar mai da ke yankin kamar Shell, Chevron, Agip da sauransu, inda mayakanta suka fasa bututan mai da dama. Wannan lamari ya shafi yawan man da kasar Najeriyar take hakowa daga ganga miliyan 2.2 zuwa ganga miliyan 1.2 a kowace rana.
A baya ma akwai wasu kungiyoyin 'yan bindiga da dama a yankin Niger Delta wadanda ke kai hare-hare kan kamfanonin mai tare da yin garkuwa da ma'aikata 'yan kasashen waje domin neman fansa, bisa abin da suka kira, fafutukar neman 'yanci. Su dai 'yan tawayen suna cewa, ba sa ci gajiyar tarin albarkatun man da ke yankin nasu.
A shekarar 2008 ne tsohon shugaban Najeriya, marigayi Umar Musa 'Yar Adua ya yiwa kungiyoyin 'yan bindigar Ahuwa da kuma sasantawa. Daga bisani aka ware musu wasu makuden kudade domin a tallafa musu.
A kwanakin baya ne kuma gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kaddamar da shirin share man da ya malala a yankin Ogoni da ke jihar Rivers a kudancin kasar ta Najeriya.
Masu sharhi dai na cewa, sabbin 'yan bindigar da suka bullo wato NDA, baya ga kungiyar MEND da kowa ya sani a baya, dukkansu akwai masu mara musu baya a boye.
Sakamakon yadda ayyukan 'yan bindigar ke gurgunta tattalin arzikin kasar, ya sa mahukuntan kasar Najeriya suka kafa wani kwamiti mai karfi da nufin hawan teburin sulhu. To, amma masu fashin baki na bayyana cewa, akwai bukatar a duba wasu daga cikin sharudan da mayakan suka gindaya. Koda yake wasu daga cikin ka'idojin nasu sun kauce hanya.
Alkaluma na nuna cewa, wadannan hare-hare sun yi matukar tasiri kan kudaden shigar kasar da ma sauran muhimman fannonin rayuwar al'ummomin kasar baki daya.
Amma hanya daya tilo ta kawo karshen wannan takaddama, ita ce hawa tenurin sulhu, maimakon yin fito-na-fito. (Ada, Ahmed, Ibrahim/Sanusi Chen)