160617-musulmin-kasar-Sin-na-azumin-watan-Ramadan-Lubabatu.m4a
|
Kamar yadda musulman sauran sassan duniya suke cikin watan azumi, daga ranar 6 ga wata ne su ma miliyoyin Sinawa musulmai a sassa daban-daban na kasar Sin suka fara Azumin watan Ramadan, wanda ake fatan kammala shi a ranar 6 ga watan Yulin wannan shekara.
Alkaluma na nuna cewa, akwai kimanin musulmai miliyan 20 a kasar Sin. Kananan kabilun kasar Sin da suka hada da Hui, Uygur, Kazakh, Uzbek, Tajik da Kyrgyz galibinsu musulmai ne suke gudanar da Azumin. Sannan ana Azumin watan Ramadan a yankuna masu 'yancin cin gashin kansu,da larduna da birane ciki har da Xinjiang, Gansu, Ningxia da kuma birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Sai a kasance tare da mu a cikin shirin, domin samun fahimtar yadda musulmin kasar Sin suke gudanar da azumi.(Lubabatu)