in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda musulmai suke Azumin Ramadan a kasar Sin
2016-06-17 16:02:08 cri

A ran 6 ga watan Yunin shekarar 2016 ne musulmai a sassa daban-daban na duniya suka fara Azumin watan Ramadan, daya daga cikin shika-shikan musuluncin nan guda biyar, wato Tauhidi, Sallah, Azumi, Rakkah da kuma zuwa aikin Hajji idan da hali.

A tsawon watan na Ramadan mai tsarki, an hana musulmai ci ko sha da yin jima'i tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana.

Bayanai na nuna cewa, an fara Azumin na bana ne a kasashe da dama na duniya kamar Najeriya, Nijar, Saudiyya, Malaysia, Indonesia, ciki har da kasar Sin mai yawan musulmai kimanin miliyan 20. Kananan kabilun kasar Sin da suka hada da Hui, Uygur, Kazakh, Uzbek, Tajik da Kyrgyz galibinsu musulmai ne suke gudanar da Azumin.

Ana kuma Azumin a kasar Sin a yankuna masu 'yancin cin gashin kansu da larduna da birane ciki har da Gansu da Ningxia da kuma birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A ranar Lahadi ne wasu manyan shugabannin gwamnatin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kanta da ke yankin arewa maso yammacin kasar Sin suka ziyarci malamai da dalibai a makarantar koyar da addinin musulunci da ke yankin, inda bayanai ke nuna cewa, akwai kimanin masallatai 24,000 da kuma sama da musulmai miliyan 13.

Kamar yadda aka saba bisa al'ada ana sa ran kammala Azumin ne a nan kasar Sin a ranar 6 ga watan Yulin wannan shekara ta 2016 da muke ciki. A cewar masana duk da banbancin lokaci, musulmai na jin dadin yin azumi a kasar Sin, ganin yadda ake tanadar da abincin bude baki da na sahur kyauta a kusan dukkan masallatai tun daga fara Azumin har zuwa karshensa da kuma ranar Sallah. (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China