160608-Buhari-ya-cika-shekara-guda-cif-a-kan-karagar-mulkin-Najeriya-Sanusi.m4a
|
Bugu da kari, Najeriya ta tsinci kanta cikin wasu tarin matsaloli, wadanda suka hada da matsalar karancin hasken wutar lantarki, da rashin aikin yi tsakanin matasan kasar, da rikicin addini da na kabilancin da kuma uwa uba matsalar cin hanci da ta zama ado a kasar.
Sai dai a lokacin da yake yakin neman zabe, shugaba Buhari ya sha alwashin kawo karshen wadannan matsaloli da suka yi wa kasar daurin kazar kuku. Sai dai wasu masu fashin baki na ganin cewa, dukkan nasarorin da jami'an tsaron kasar ke cewa suna samu a kan mayakan Boko Haram, wannan tamkar baya ba zane ne, domin a daya bangaren kuma matsalar sace mutane ana garkuwa da su domin neman fansa da kuma yadda tsagerun yankin Niger Delta ke ci gaba da fasa bututan mai a yankin na ci gaba da tsananta.
Haka za kila, yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki shi ma batu ne da ke damun 'yan kasar, lamarin da masana ke cewa, ya faru ne sakamakon faduwar farashin mai da kasar ta dogara a kai a kasuwannin duniya da kuma yadda ake fasa na'urorin kamfanonin hakar mai a yankin Niger Delta da sauransu.
Masu sharhi na cewa, shugaba Buhari ya taka rawar gani a fannonin inganta tsaro da kuma manufofin gwamnatinsa na samar da ayyukan yi ga matasan kasar. Don haka, kamata ya yi 'yan kasar su kara yin hakuri tare da baiwa shugaban goyon baya da karin lokaci, ganin irin tarin matsalolin da ya gada da kuma halin da duniya ke ciki ta fuskar tattalin arziki. (Ada, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)